Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kaddamar da Kwamitin Shirye-shiryen Bikin Cika Shekaru 37 da Kafuwar Jihar
- Katsina City News
- 09 Sep, 2024
- 215
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times Satumba 9, 2024
A wani bangare na shirin cika shekaru 37 da kafuwar Jihar Katsina, Sakataren Gwamnatin Jihar, Barista Abdullahi Garba Faskari, ya kaddamar da wani kwamitin manyan jami’ai da aka dora wa alhakin tsara bikin da ke tafe. An kafa kwamitin ne bisa umarnin Gwamnan Jihar Katsina, don duba ci gaban da aka samu, abubuwan da ake aiwatarwa a yanzu, da kuma shirye-shiryen gaba na jihar.
A jawabinsa yayin bikin kaddamar da kwamitin, Barista Faskari ya ja hankalin mahalarta kan muhimmancin ranar 23 ga watan Satumba, 1987, ranar da aka kafa Jihar Katsina. "Cikar shekaru 37 yana ba mu damar kimanta abubuwan da muka cimma, abinda muke yi a yanzu, da kuma shirin mu na gaba," in ji shi.
Barista Faskari ne ke shugabantar kwamitin, wanda ke kunshe da manyan jami’an gwamnati daga ma’aikatun daban-daban. Cikin mambobin kwamitin akwai Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, Antoni Janar kuma Kwamishiniyar Shari'a ta Jihar, da kwamishinonin muhimman ma’aikatu irin su Ayyuka, Gidaje da Sufuri, Kasa da Tsare-tsaren Birane, Yada Labarai da Al’adu, da Harkokin Mata. Kowace ma’aikata za ta taka muhimmiyar rawa wajen shirin bikin, tare da samun ikon shigar da wasu karin mambobi idan an ga dama domin tabbatar da nasarar taron.
An dorawa kwamitin alhakin tsara bikin yadda zai kasance cikin tsari da nasara, gami da tantance abubuwan da za su gudana, bakin da za a gayyata, da yadda za a gabatar da tarihin jihar da shirinta na gaba. "Mun kuduri aniyar gudanar da biki mai kayatarwa da zai nuna irin nasarorin da jihar ta samu da kuma shirin ta na gaba," in ji Barista Faskari.
A wajen Kaddamar da kwamitin Faskari yayi kira ga dukkan sassan gwamnati da masu ruwa da tsaki su bayar da hadin kai domin tabbatar da nasarar bikin. An shirya gudanar da bikin ne a ranar 23 ga Satumba, 2024.