GINA FAMFUNAN TUƘA-TUƘA A SAKKWATO KAN NAIRA BILIYAN 1.2, TSAKANIN SANI DA RASHIN SANI
- Sulaiman Umar
- 08 Sep, 2024
- 338
Daga Alkalamin Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali Kano:
A kwanakin baya gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Dakta Ahmad Aliyu ya yi wata magana kan haƙa rijiyar borehole amma adadin kuɗin da ya faɗa sai aka yi masa ca aka fara yada farfaganda har abin ya zama abin zolaya ga wadanda suka jahilci mai gwamna yake nufi da abin da gwamna zai yi.
Faɗin za a yi borehole masu ƙaramin sani sai suka ɗauka borehole ce irin wanda aka saba yi a gidana da gidanka. Injiniyoyin kirki da yake sana’arsu ce haka borehole ka ji sun yi magana? To ba su ce komai ba saboda sun san borehole kala-kala ce kuma kuɗi–kuɗi ce ta danganta da ina za a gina ta da wanda zai gina ta da kuma amfanin da za ta yi. Wato waɗanda za su amfana da ita.
Bari na ba ku misali.
Borehole irin ta gidanka da gidana in za a yi ta ana haka ta ne ko dai a cikin gida ko a waje kuma ta ba wa cikin gida ruwa da yan fanfuna a kofar gida. Wannan ba za ka hada kuɗinta da borehole ɗin da za ka yi wanda za ta ba wa unguwa ko gari ruwa ba.
Ana borehole ɗin zamani mai aiki da solar da panel. Shi kansa panel din ya danganta daga ɗaya har 100. Bayan panel akwai tankuna na karfe da karafunan da ake ɗora tankin, duka suma kuɗi ne wanda kai Mista lay man ba ya cikin tsarin borehole dinka mai karamin ƙarfi.
Daga inda za a yi borehole ɗin zuwa inda za a janyo a kai ruwan ka san mita nawa ne? ba ka da wannan adadin amma ka ke jayayya akan kudin? Ba na mantawa a Kano a shekarun baya an taba irin wannan cecekucen akan za a yi borehole a Audu Baƙo secretariat akan kuɗi miliyan ishirin da bakwai a ma wancan lokacin kuma ko a lokacin da aka fito da kuɗin dalla-dalla sai aka ga ma sai an yi ciko, bare a naira irin ta yau ko dala irin ta yau.
Hatta a pipe da za a saka, zurfinsa a borehole da ake yi a gida ba ya fin mita hamsin zuwa sittin kuma a samu ruwa wanda zai isa bukatun mutanen gidan. Ba za ka haɗa kuɗinsa da irin wannan borehole ɗin da gwamnan Sakkwato yake bayani ba wanda za a yi mita ɗari biyu har zuwa ɗari hudu a ƙasa saboda adadin waɗanda za su amfana da ruwan da iya nisan da ake son a kai ruwan da kuma karko ko quality na aikin da ake bukata ruwan ya kai don amfanin al’umma. A dai bangaren pipe din dai , shi ma inci -inci ne don haka irin wannan pipe din ana amfani da five inches ne mai makon pipe mai inci daya ko biyu da ake amfani da su a kananan borehole. Kada kuma a manta wurin da za a yi irin wannan borehole Yana da bambanci daga wuri zuwa wuri. Sokoto kowa yasan tana kusa da Sahara don haka inda za a haka a samu ruwa yana da bambanci da inda za a yi a Kano ko Jigawa ko Bauchi. Hatta motocin da suke haka borehole din sun bambanta da wadda ake yi a wasu jihohi da garuruwa.
Don haka, don an ce za a yi borehole kan 1.2 Billion guda ishirin da hudu bai kamata ya zama abin surutu da ce-ce-ku-ce ba, kamata ya yi a tsaya a ga wanne irin borehole za a yi tukunna. Ya kamata adawar siyasa da ma waɗanda su ba adawar suke ba fatansu kawai su ga kuskure su yaɗa ya kamata su jira. Bahaushe yana cewa “komai gaggawar Ungozoma ta jira dai a haihu” don haka Ahmad Aliyu a dai yanzu yana kan aiki bai yi kuskure ba a faɗin za a yi sababbin borehole ne da kuɗin kuma za a yi masu inganci ne da nisan zango. Hatta pump machine za a yi amfani da grundfos submersible pump series five ne AC DC don haka yana da bambanci da Wanda ake amfani da shi yau da gobe a gidaje da unguwa.Da kyakkyawan fatan duk inda matsalar ruwa take in dai waɗannan borehole sun tabbata to za a yi sallama da matsalar da yardar Allah. Allah ya sa mu dace, amin.