Katsina: Cibiyar Bada Agajin Gaggawa Ta “RED CROSS” Ta Gudanar Da Bitar Wayar Da Kai Ga Masu Ruwa Da Tsaki Kan Bada Taimakon Gaggawa Ga Marasa Lafiya
- Sulaiman Umar
- 03 Sep, 2024
- 346
Daga Sulaiman Ciroma
Cibiyar nan mai bada agajin gaggawa ga marasa lafiya a matakin farko wacce aka fi sani da “RED CROSS” ta gudanar da bitar wayar da kai game da yanda ake bada agajin gaggawa wato “First Aid” ga masu ruwa da tsaki a jihar Katsina.
Bitar wanda aka shirya shin a tsawon kwana biyu daga Asabar 31 ga Agusta zuwa Lahadi 1 ga watan Satumba ya samu halartar masu ruwa da tsaki musamman jami’an hukumomin tsaro daga bangarori daban-daban duba da yanda lamarin ya shafe su.
Cikin mahalarta taron akwai jami’an sojoji, ‘yan sanda, immigration, Road safety, NSCDC, Fire Service, Katsina State Hisbah Board da dai sauransu.
A yayin taron an tattauna batutuwa masu muhimmanci da dama musamman wayar da kai ta yanda za a bada taimako ga marasa lafiya ko mai rauni a matakin farko kafin mika shi izuwa asibiti.
Cikin abubuwan da aka koyar, an koyar da yanda za a taimaki mai rauni kamar ciwon da ke zubar da jini ta yanda za a taimaka wajen tsayar da jinin da kuma yanda za a taimaki mai lalurar karaya ko harbin maciji da duk wani nau’in ciwo da ke bukatar taimakon gaggawa kafin zuwa asibiti da kuma hanyoyi da dama da ake daukar marasa lafiya.
Kadan daga cikin hotuna yayin gudanar da taron: