Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina Ta Kama Mashahuran Masu Laifi Uku: Dillalin Kwayoyi, Barawon Babur, da Mai Satar Wayoyin Wutar Lantarki
- Katsina City News
- 27 Aug, 2024
- 447
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Rundunar 'Yan Sanda ta Jihar Katsina ta sanar da kame wasu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, Kakakin Rundunar, ASP Sadiq Abubakar, ya bayyana irin nasarorin da rundunar ta samu a taron manema labarai da aka gudanar a Hedikwatar Rundunar, ranar Talata 27 ga watan Agusta
A ranar 23 ga Agusta, 2024, misalin karfe 06:00 na safe, jami'an 'yan sanda na Sabangarin Katsina sun kama wani da ake zargi mashahurin dillalin miyagun kwayoyi, mai suna Salisu Jibril, mai shekara 35, mazaunin garin Oni 'Yasu a karamar hukumar Rimi. Bisa sahihan bayanan sirri, 'yan sandan sun gano Ƙumshin kwayoyi 1,330 na Exalt da Tramadol da kuma fakiti 15 na Lara a hannun wanda ake zargin. A halin yanzu, ana ci gaba da bincike a kan wanda ake zargin kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.
A wani samame daban da aka gudanar a ranar 15 ga Agusta, 2024, misalin karfe 10:00 na safe, rundunar ta kama wani da ake zargi mashahurin barawon babur, mai suna Abdullah Haruna, yayin da yake kan hanyar Jibiya zuwa Katsina. Wanda ake zargin, mazaunin Kauyen Karam-bana, dake karamar hukumar Dutsinma, an same shi da babur din da ake zargi an sace. Bincike na farko ya bayyana cewa Haruna yakan bawa wadanda yake son ya saci babur dinsu maganin shaye-shaye ko abinci da aka cakuda da kayan maye, inda sukan fita hayyacinsu kafin ya tafi da babur din domin sayarwa. Ya kuma amsa cewa ya hada kai da wani abokin huldarsa, Alhaji Sa'idu, wanda a halin yanzu ake nema ruwa a Jallo. Inda rundunar ta himmantu wajen ganin an kamo abokin ta'asar nasa.
A yau, 27 ga Agusta, 2024, misalin karfe 1:00 na rana, jami'an 'yan sanda sun kama wani matashi mai shekara 18 mai suna Aliyu Aliyu, Dan'asalin karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara. An kama Aliyu da laifin satar wayoyin wutar lantarki. An kama wanda ake zargin da wayoyin wutar lantarki da ake zargi an sace a wani gida dake kauyen Natsinta a jihar Katsina. Wanda ake zargin ya amsa cewa ya hada kai da wani mutum mai suna Shamsu Musa, mazaunin unguwar Zonguna a nan Katsina, wanda a halin yanzu ya tsere ana kan nemansa don gurfanar da su a gaban shari'a.
ASP Sadiq Abubakar ya jaddada kudirin rundunar na ci gaba da tabbatar da doka da oda a jihar Katsina, tare da tabbatar wa jama’a cewa za a ci gaba da kama dukkanin masu laifi da hana aikata miyagun laifuka.