Sabon Shugaban Hukumar Hajji Ta Kasa Ya Kai Ziyara Ga Gwamnan Jihar Katsina
- Katsina City News
- 27 Aug, 2024
- 486
A ranar Talata, 27 ga watan Agusta 2024, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D., CON, ya karɓi bakuncin Sabon Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, a ofishinsa domin ziyarar sada zumunci.
Farfesa Pakistan, wanda ɗan asalin ƙaramar Hukumar Mai'adua ce a Jihar Katsina, ya kawo ziyarar ne domin sada zumunci da neman shawarwari kan sabon mukamin da aka ba shi.
Yayin ganawar, Farfesa Pakistan ya bayyana jin dadinsa da dawowa gida, domin ya kasance ɗan asalin Jihar Katsina. Ya kuma nemi goyon bayan Gwamnan tare da shawarwari domin ya samu damar sauke nauyin da ke wuyansa.
A nasa ɓangaren, Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyara, yana mai addu’ar fatan alkhairi ga Farfesa Pakistan a sabon mukaminsa. Haka kuma, Gwamnan ya yaba da zabin da Shugaban Ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi na naɗin Farfesa Abdullahi Pakistan.
A yayin wannan ziyarar, Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Hon. Faruq Lawal Jobe, da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, Hon. Jabiru Abdullahi Tsauri, sun halarci taron. Hakanan, tawagar da ta rakashi ta haɗa da Mai ba Gwamna shawara kan harkokin siyasa, Hon. Ya’u Umar Gwajo-Gwajo, da Ɗan Majalisar Jiha mai wakiltar Karamar Hukumar Mai'adua, Mustapha Rabe Musa, da Shugaban Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Jihar Katsina (NULGE), Alh. Nasiru Wada Mai'adua.