Gwamnan Katsina Zai Kaddamar da Kwamitocin Raya Kasa Don Inganta Makomar Al'ummar jihar Katsina

top-news

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa an kammala shirye-shirye na kafa kwamitocin raya al'umma a dukkan kananan hukumomi 34 na jihar. Manufar wannan shirin ita ce inganta cigaban al’umma ta hanyar bai wa mazauna garuruwa damar tantance ayyukan da suka fi muhimmanci a gare su.

Gwamna Radda ya bayyana hakan ne yayin ganawa da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, wanda ya jagoranci tawagar da ta tarbe shi bayan dawowarsa daga hutun shekara guda na wata daya da kuma tafiyar aiki ta kwana biyar a kasar Sin.

Hakazalika, don tabbatar da cewa manufofin gwamnati sun dace da bukatun da muradun jama’a, Gwamnan zai shirya tarukan ganawa da al'umma a dukkan mazabu uku na sanatan jihar. Wadannan taruka za su bayar da dama ga mahukunta, ciki har da ‘yan majalisar jiha da na tarayya, da kuma ‘yan hamayya, su gabatar da ra’ayoyi da shawarwari.

Yayin da ya jaddada muhimmancin hadin kai a cikin al'umma, Gwamna Radda ya bukaci dukkan shugabanni da aka zaba su yi aiki tare da shugabannin addini don yin addu'o'in samun zaman lafiya a jihar. Haka kuma, ya yi kira gare su da su rungumi rayuwa mai sauki tare da kasancewa kusa da jama’arsu, musamman a wannan mawuyacin lokacin tattalin arziki.

Tun da farko, yayin da yake tarbar Gwamnan, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Hon. Nasiru Yahya Daura, ya yaba da jagorancin mataimakin gwamnan a lokacin zanga-zangar da aka yi a fadin kasa kwanan nan. Haka kuma, ya bayyana kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta tare da alkawarin ci gaba da ba da goyon bayan Majalisar wajen magance wadannan matsaloli.

NNPC Advert