An Kaddamar Da "Kungiyar Kiran Kawo Gyara Da Ci Gaban Kasa Ta Nijeriya" A Matakin Jiha A Katsina.
- Katsina City News
- 25 Aug, 2024
- 243
Kungiyar nan ta "Kira Ga Kawo Gyara Da Ci Gaban Kasa A Nijeriya" wato 'Advocacy For Integrity & Rule Of Law Initiative (AIRLIN)' a turance, ta yi taron kaddamar da Ofishinta na jihar Katsina.
Taron kaddamarwar wanda ya gudana a dakin taro na Kungiyar ma'aikatan Lafiya ta jihar Katsina, dake Goruba road ya samu halartar mutane daban-daban musamman Matasa.
Tun farko da yake Jawabi a taron, Shugaban kungiyar na Kasa, Malam Ibrahim Muhammad Gamawa ya yi tsakure a kan yadda turbar kasar Nijeriya ta taho a tarihi, da yadda shugabannin farko suka riki kasar da kishi da amana, da yadda ya zuwa yanzu abubuwa suka ta6ar6are, inda ya bayyana hakan a matsayin tunanin samar da wannan kungiya tashi a matsayin ta bada gudummuwa wajen kawo gyara da ci gaban kasar.
Malam Gamawa, ya kuma zayyano wasu daga cikin kudurorin kungiyar da suka hada da: yakar miyagun dabi'u kamar shan miyagun kwayoyi, Tukin ganganci, kimanta al'adunmu masu dauke da tarbiyya da aminci a tsakanin juna, da wayar da kai dangane da dukkan ayyukan da suka kaucewa Doka da Oda.
Auwal Abba Yahaya, shi ne shugaban kungiyar a Matakin Jiha, shi ma ya yi karin haske kan dalilan samar da kungiyar da za ta tsayu kai da fata cikin hukuncin Ubangiji don kawo gyara ga al'umma, inda ya zayyano: Halin da kasa take ciki, koma bayan Matasa ta kowace fuska, bukatuwar taimaka wa hukumomi, a matsayin wasu abubuwan da ke kawo tsaiko wajen ci gaban kasarmu Nijeriya.
Taron dai ya samu halartar dukkanin Koodinetoci na kananan hukumomi 34 dake fadin jihar Katsina, Jami'an gwamnati, Jami'an tsaro, 'Yan Jarida da sauran al'umma.
Hakazalika duk a taron, Malamai masana daga 6angarorin Ilimi sun gabatar da jawabai a wajen. Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi a taron akwai Farfesa Sani Abdu Fari daga jami'ar Umaru Musa 'Yar'adu, Dr. Ibrahim Isa Gani da sauransu.
Bugu da kari duk a taron, an bude filin tambaya da amsa dangane da kungiyar da manufofinta, sannan daga bisani aka kaddamar da shugabannin kungiyar a matakin kananan hukumomi guda 34 da Shugabannin na jiha, gaba daya.