Ahmed Rufa'i Abubakar Ya Yi Bayani Kan Ajiye Muƙamin sa na Shugaban hukumar Leken Asiri A Nijeriya
- Katsina City News
- 24 Aug, 2024
- 363
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A wata hira da aka yi da Ambasada Ahmed Rufai Abubakar, Sardaunan Katsina, shugaban NIA a gidan talabijin na Ƙasa (NTA) jim kadan bayan ya ajiye aikinsa, Ahamed Rufa'i ya bayyana dalilansa na yin murabus tare da tsokaci kan lokacin da ya yi yana hidima. Ambasada Abubakar ya godewa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bisa damar da ya ba shi na hidimtawa Najeriya karkashin jagorancin sa.
“Abu ne na yau da kullum in rika yiwa Shugaban Kasa bayani kan wasu abubuwa da batutuwa, kuma yau ba a bar baya a gaba ba. Bayan na gama bayani, sai na gabatar da murabus dina, kuma Shugaban Kasa ya amince da shi cikin mutunci,” in ji Ambasada Ahamed Rufa'i.
Ya jaddada muhimmancin damar da ya samu na yiwa shugabanni biyu aiki a jere ba tare da tsayawa ba, inda ya bayyana lokacin watanni 15 da ya yi yana hidima karkashin gwamnatin Shugaba Tinubu. Ambasada Abubakar ya tabbatar da ci gaba da hidimtawa Najeriya a wata hanya ta daban, duk da cewa ya ajiye aikinsa.
Da aka tambaye shi game da tambayoyin da mutane ke yi kan dalilin yin murabus dinsa, Ambasada Abubakar ya ce ba wani abu mai tsanani ya haifar da wannan murabus din ba, yana mai alakanta hakan da batutuwan sirri da na iyali. Ya kuma tabbatar da cewa abokantaka da girmamawa tsakanin sa da Shugaba Tinubu za ta ci gaba da kasancewa.
Ahamed Rufa'i ya kuma bayyana irin tattaunawar da suka yi da Shugaba Tinubu, inda Shugaban ya fahimci matsayinsa tare da yaba gudummawar da ya bayar. Ambasadan ya nuna matukar godiya bisa amincewa da ya samu daga Shugaba Tinubu, musamman a fannin tsaron kasa.
Yayinda yake tunawa da lokacin da ya yi a mukaminsa, Ambasada Ahamed Rufa'i Abubakar ya ce, “Karfin gwiwar da na samu, amincewar da ya yi mini da kuma hidimar da na yi, damar da aka ba ni na saurare na, karanta bayanan da na gabatar da shawarwari, duk sun kasance abin alfahari gare ni.”
Yayinda yake kammala hirar, Ambasada Abubakar ya bayyana jin dadinsa kan horar da matasan ma’aikatar da jami’ai tsawon shekaru bakwai da ya yi yana aiki a matsayin Darakta-Janar, a hukumar leken Asiri, yana mai tabbatar da cewa an horar da kwararrun jami’ai da dama wadanda za su iya ci gaba da aiki da kyakkyawan tsari.
Murabus din Ambasada Ahamed Rufa'i Abubakar ya kawo karshen wani babban babi a aikinsa mai tarin daraja, amma babu shakka baya da ya bari na hidima da sadaukarwa ga Najeriya za su ci gaba da kasancewa, a cikin Alfahari.