Gwamnatin Katsina Ta Bayyana Matsayar ta Akan Matakin Kare Kai.
- Katsina City News
- 22 Aug, 2024
- 449
Maryam Jamilu Gambo, Katsina Times
Gwamnatin Jihar Katsina, karkashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, ta bayyana matsayinta kan tattaunawar da ake yi game da matakan tsaro na al’umma. Akasin rahotannin da ke nuni da cewa an ba wa ‘yan ƙasa umarni su mallaki makamai domin kare kansu daga ‘yan bindiga, gwamnatin ta jaddada cewa ba ta fitar da wani umarni na a sayi makamai ba.
Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Al’umma, Dr. Nasir Muazu, ya bayyana cewa matakin gwamnatin ya ta’allaka ne kan tsari na gaggawa, musamman ga ƙananan hukumomi takwas da ke fuskantar matsalolin tsaro sosai. Maimakon goyon bayan mutane su mallaki makamai da kansu, gwamnatin ta kafa Kungiyoyin Sa-kai na Al’umma (CVG) waɗanda ke da alhakin kare al’ummominsu.
A cewar Dr. Muazu, an tsaurara tantancewa da horar da waɗannan kungiyoyin kan yadda za su kare kansu, kuma an ba su bindigogin farauta na Dane, waɗanda doka ta amince da su a Najeriya. Kungiyoyin suna aiki ne a matsayin matakin tsaro na farko a yankunan da za su ɗauki lokaci kafin jami’an tsaro su isa.
“Wannan shiri yana nufin ba wa mazauna yankunan ilimi da kayan aiki da za su inganta tsaronsu, wanda hakan zai rage yawaitar hare-haren ‘yan bindiga,” in ji Dr. Muazu. Haka kuma, ya jaddada cewa wannan shirin yana nuna karfin gwamnatin na haɗa jama’a a cikin yaƙi da rashin tsaro.
Gwamnatin Jihar Katsina ta sake jaddada aniyarta na tabbatar da tsaro da zaman lafiya ga dukkan ‘yan jihar, tare da tabbatar da ci gaba da haɗin kai da hukumomin tsaro na tarayya domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk faɗin jihar.