Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Katsina Ta Ƙarfafa Alaƙa da Ma'aikatar Shari'a da 'Yan Sanda
- Katsina City News
- 21 Aug, 2024
- 376
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 21 ga Agusta, 2024:
Shugaban Hukumar Jin Ƙorafe-Ƙorafen Jama'a da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Katsina, Mai Shari'a Lawal Garba Abdulkadir (mai ritaya), ya ƙara ƙaimi wajen ƙarfafa haɗin kai da hukumomin tsaro a faɗin jihar. A cikin jerin ziyarce-ziyarce da hukumar ta gudanar, Mai Shari'a Abdulkadir tare da tawagarsa sun gana da manyan jami'ai a bangarorin shari'a da 'yan sanda domin kulla kyakkyawar alaƙa da nufin inganta aikin hukumar.
A yayin ziyarar da suka kai Ofishin Girandi Kadi na Jihar Katsina, Mai Shari'a Muhammad Kabir Abubakar, tawagar ta nemi haɗin kai tare da nuna alaƙar da ke tsakanin ayyukansu. Mai Shari'a Abubakar ya yabawa gwamnatin Jihar Katsina bisa kirkiro da wannan hukuma, inda ya tabbatar da cewa tana da manyan ƙalubale. Ya kuma ja hankalin tawagar da su mayar da hankali wajen tunkarar waɗannan ƙalubalen domin cimma nasara.
A wata ziyara zuwa Babban Ofishin 'Yan Sandan Jihar Katsina, Mai Shari'a Lawal Garba Abdulkadir da tawagarsa sun gudanar da tattaunawa kai tsaye da Kwamishinan 'Yan Sanda, CP Aliyu Musa. Sun gabatar masa da kundin dokar da ta kafa hukumar, tare da neman ƙarin haɗin kai a manyan fannoni na hadin gwiwa.
CP Aliyu Musa ya bayyana jin daɗinsa game da ziyarar kuma ya yaba da ƙoƙarin hukumar. A cikin jawabinsa, CP Musa ya jaddada muhimmancin haɗa hannu da tsoffin jami'an 'yan sanda da suka yi ritaya a cikin hukumar, inda ya bayyana cewa za su taimaka sosai wajen sauƙaƙa wasu ayyuka. Ya kuma yi alkawarin samar da dukkanin tsaron da hukumar ke buƙata, ciki har da tsaro ga ma'aikatan gida da ofisoshinsu.
CP Musa ya kammala da nuna tabbacin sa game da cancantar shugabancin hukumar da kuma ƙwarewar da za su bayar wajen jagorantar 'yan sanda domin inganta bincike da gabatar da ƙara. Ya tabbatar da cewa za a ci gaba da ba da goyon baya da haɗin kai, tare da ware ƙwararrun lauyoyi da masu bincike don taimaka musu a ayyukansu.
Waɗannan ziyarce-ziyarce sun zama muhimmin mataki a cikin burin Hukumar Jin Ƙorafe-Ƙorafen Jama'a da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Katsina na gina kyakkyawar alaƙa da manyan hukumomin tsaro a cikin jihar, domin samun haɗin kai mai ƙarfi wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma ƙara ƙarfin gwiwar jama'a ga ayyukan gwamnati.