Hukumar Korafe-korafen Jama'a da Yaƙi da Cin Hanci Da Rashawa Ta jihar Katsina Ta Nemi Hadin Kan Ma'aikatar Shari'a
- Katsina City News
- 15 Aug, 2024
- 232
A ranar Alhamis 15 ga watan Agusta ne Hukumar ta Jin Korafe-korafen Jama'a da hana cin hanci da rashawa ta jihar Katsina ta kai ziyara a ma'aikatar Shari'a da Ofishin Babban Jojin jihar Katsina don neman hadin gwiwa don gudanar da Ayyukan hukumar a cikin Nasara.
Ziyarar a karkashin jagorancin shugaban hukumar Justice Lawal Garba (Mai Ritaya) ya bayyana bukatar samar da hadin kai da goyon bayan ma'aikatun biyu don gudanar da aiki tare a cikin Nasara. A inda ya gabatar da wasu bukatu a ofishin ma'aikatar Shari'a don duba su tare da aiwatar da su duba da ita hukumar tana karkashin Ma'aikatar shari'a.
A jawabin ta Babbar Jojin jihar Katsina Mai Kwamishinar Shari'a Barista Fadila Muhammad Dikko ta jinjina wa hukumar tare da gwamnatin jihar Katsina karkashin jagoranci gwamna Radda bisa samar da ita tare da zabo jajirtataccin mutane kuma masana shari'a da zasu gudanar da hukumar.
A karshe Kwamishinat ta tabbatar da bawa hukumar hadin kai da samar ma hukumar wasu abubuwan bukatu nan kusa-kusa duba da hukumar sabuwa ce.
A nasa jawabin babban jojin jihar Katsina mai Shari'a Musa Danladi Abubakar ya yaba wa kwazon Justice Lawal Garba inda kuma yayi kira ga jajircewarsa tare da bada hadin kai dari bisa dari. Danladi Abubakar ya yi karin haske akan cewa gwamna da mataimakin sa kadai ke da rigar kariya don haka dole ne a sa ido don tabbatar da hukumar tayi aikinta akan duk wanda yayi ba daidai ba.