Na Aikata Zina Da Sama Da Maza 3000 A Rayuwata, Inji Wata Jarumar Fim
- Sulaiman Umar
- 13 Aug, 2024
- 521
Esther Nwachukwu ta kasance jarumar fina-finai ce a Najeriya wacce aka fi sani da Esther Sky, a inda ta bayyana sirrin nata na boye a game da sana’ar karuwanci.
A cikin wani shiri na kwanannan mai taken ‘The Honest Bunch Podcast,’ shahararriyar jarumar mai suna Esther Nwachukwu ta bayyana cewa ta aikata zina da sama da maza 1000 daga kasashe daban-daban.
Jarumar wacce ta ke haifaffiyar jihar Imo ta kara da cewa tana saduwa (Zina) ne kawai da mazajen aure sakamakon sun fi dadin sha’ani da kuma samun fahimtar juna sabanin samari.
“Jikina na daukan maza sama da 1000, Sannan nayi zina da maza sama da 1000 yayin da na cike shekaru 30 da haihuwa a 7 ga watan July,” Inji Esther.
“Na mance yawan mazajen da nayi zina dasu, bama zan iya tunawa ba. Na sadu da maza sama da 3000. Wadanda daga cikinsu akwai ‘yan Nigeria, Cyprus, Turkiyya, Kenya da kuma Ghana.
“Bana aikata zina da samari, ina yi ne kawai da mazajen aure saboda sun fi dadin sha’ani sannan munfi samun fahimtar juna. Bugu da kari kuma mazajen aure basa dadewa yayin jima’i don kada karfinsu ya kare su kasa tabuka komai ga matayensu na gida.”
Esther Nwachukwu wacce tayi karatu a Lagos Polytechic (LASPOTECH), ta ba da hujjar cewa mata masu sana’ar karuwanci sune matan da ya dace a aura sakamakon yin nadamar abinda suka aikata a baya.
“Matan da suka fi dacewa a aura a wannan zamanin sune karuwai saboda su ke da ilimin mazakutan mazaje daban-daban sakamakon sun ga jiya sun kuma ga yau. Saboda haka da ka auri karuwa, to fa baza ta taba cin amanarka ba saboda ta riga da ta sadu da maza da dama kafin kai,” Inji ta.
Jarumar ‘yar jihar Legas ta kasance shahararriya a fannin shirya fina-finai a Asaba na jihar Delta.