Gwamna Radda Ya Amince da Farfado da Cibiyar Koyon Harshen Faransanci a Katsina
- Katsina City News
- 10 Aug, 2024
- 187
Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda, tare da hadin gwiwar shirin AGILE, ta gyara makarantar Bilingual ta Katsina da ke SUNCAIS, cikin garin Katsina.
Haka kuma, Gwamna Radda ya amince da farfado da cibiyar koyon harshen Faransanci da za ta ci gaba da gudanar da karatu a makarantar, wanda zai shafi shirye-shiryen takardun shaidar kammala karatu da kuma wasu kwasa-kwasan ilimin harshen Faransanci.
Cibiyar Koyon Harshen Faransanci da ke cikin jihar Katsina tana da fa'idojin ilimi masu yawa, ciki har da samun damar tallafin karatu ga daliban Katsina don yin karatu a kasar Faransa, bayar da kwasa-kwasai, bita, da shaidar kammala karatu a fannin harshen Faransanci, adabi, da al'adu, da kuma samar da sha'awa wajen aiki a hukumomin duniya, diflomasiyya, da sauransu.
Bugu da kari, wannan cibiya za ta samar da damar koyon harshen Faransanci da al'adunsa, da bunkasa kwarewar sadarwa don hulda da kasa da kasa, tafiya, da harkokin kasuwanci.
Wannan matakin zai kawo ci gaba sosai a bangaren ilimi a Jihar Katsina sakamakon kyakkyawar jagorancin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda.