Gwamnatin Katsina Ta Kaddamar da Kwamitin Bincike kan Ayyukan Hisbah
- Katsina City News
- 23 Jul, 2024
- 468
Gwamnatin Jihar Katsina ta kaddamar da kwamitin da zai binciki ayyukan hukumar Hisbah a jihar. Sakataren Gwamnatin Jihar, Barr. Abdullahi Garba Faskari, ne ya kaddamar da kwamitin a ranar Litinin, 23 Yuli, 2024, a ofishinsa dake Sakatariyar Jihar Katsina.
Yayin kaddamar da kwamitin, Barr. Faskari ya bayyana cewa kafa kwamitin ya biyo bayan rahoton da gwamnati ta samu na faifen bidiyon yadda jami'an Hisbah ke gudanar da aikinsu. Kwamitin, wanda ke da mambobi shida, zai kasance karkashin jagorancin Kwamishinan Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Jihar Katsina, Hon. Aliyu Lawal Zakari.
Mambobin kwamitin sun hada da: Sakatare na dindindin na Ma’aikatar Addinai, Sakatare na dindindin na Ma’aikatar Shari’a, Sakatare na dindindin na Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida, da wasu kwararru.
A jawabin sa, Hon. Zakari ya tabbatar da cewa kwamitin zai gudanar da bincike cikin tsanaki, tare da mika rahoton ga gwamnati cikin lokaci.
Kwamitin zai mayar da hankali kan abubuwa kamar binciken gaskiyar faifen bidiyon da ake yadawa a shafukan sada zumunta, nazarin dokar da ta kafa hukumar Hisbah, da kuma gano duk wani abu da ke haifar da take hakkin bil'adama.