Ibo Sun Goyon Bayan Shugaba Tinubu, Ba Za Su Yi Wani Zanga-zanga Ba – Umahi
- Katsina City News
- 18 Jul, 2024
- 402
Katsina Times
Gabanin zanga-zangar kasa baki daya a Najeriya kan matsalolin tattalin arziki, Ministan Ayyuka, David Umahi, ya ce yankin Kudu maso Gabas na Najeriya ba zai kasance cikin wata zanga-zanga kan Shugaba Bola Tinubu ba.
Umahi ya kuma bayyana cewa gwamnatin Shugaba Tinubu na daukar matakai masu wahala don dawo da martabar kasar da ta bata.
Umahi ya bayyana haka ne a Abakaliki ranar Laraba yayin taron tuntuba na masu ruwa da tsaki game da daidaitawar aikin gina hanyar superhighway mai tsawon kilomita 477 daga Cross River-Kudu maso Gabas-Arewa ta Tsakiya-Apo Abuja, ciki har da kilomita 101 na Jihar Ebonyi.
Ya gargadi wadanda ke tayar da zaune tsaye a kasar da su daina, domin hakan bai da wani amfani.
Ya bayyana cewa mutanen Kudu maso Gabas ba su cikin wani hatsari, kuma su guji zaman gida saboda yadda yake lalata tattalin arziki da kuma jefa kai cikin wahala.
Ministan Ayyuka ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su goyi bayan manyan ayyukan Bola Tinubu, yana mai bayanin cewa hanyar gabar teku na zuwa da manyan fa'idodin tattalin arziki da suka shafi kasar gaba daya.
Babban abin birgewa a taron shine kaddamar da aikin gina hanyar gabar teku ta uku, Lagos-Calabar Coastal Highway, wanda ya hada da yankunan Ebonyi, Enugu, Benue, da Abuja.