Gwamnatin Jihar Katsina Tare da UNDP da WANEP Sun Tallafawa Mata 300 a Kaita da Faskari
- Katsina City News
- 11 Jul, 2024
- 495
Maryam Jamilu Gambo, Katsina Times
Gwamnatin jihar Katsina tare da hadin gwiwar shirin ci gaban zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) da cibiyar gina zaman lafiya ta Afirka ta Yamma (WANEP), sun tallafawa mata daga ƙungiyoyin haɗin gwiwa 300 a ƙananan hukumomin Kaita da Faskari.
Shirin mai taken "Tsarin Zaman Lafiya Don Gina Tsaftace Rayuwar Al’umma a Jihar Katsina" ya samar da kayayyakin Amfanin gonada da Sana'o,i don bunkasa karfin tattalin arzikin mata da kuma inganta dogaro da kai.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ne ya kaddamar da rabon kayayyakin a cibiyar mata ta Multif-Purpose, Filin Samji, cikin birnin Katsina.
Da yake jawabi ga mahalarta taron game da muhimmancin shirin, Gwamna Radda ya ce, "Wadannan kayayyaki suna da muhimmanci wajen bunkasa 'yancin tattalin arziki da ci gaba mai ɗorewa ga mata."
Gwamna Radda ya yaba wa UNDP da WANEP bisa haɗin gwiwar da suka yi, inda ya nuna cewa wannan tallafi ya zo a daidai lokacin da jihar ke matukar bukatarsa.
Kwamishiniyar harkokin mata, Hajiya Zainab Musa Musawa, ta bayyana cewa kayayyakin da aka bayar sun haɗa da takin zamani, famfunan ruwa, injunan sarrafa shinkafa da injunan tsabtace shinkafa. Sauran kayayyakin sun haɗa da injunan noman rani da injunan niƙa.
Hajiya Musawa ta bayyana cewa waɗannan kayayyaki za su ba wa mata damar bayar da muhimmiyar gudunmawa ga al’ummominsu da kuma haifar da ci gaba mai ɗorewa.
Tun da farko, Injiniya Bello Lawal Yandaki, shugaban ƙungiyar shugabannin kananan hukumomi (ALGON), ya yi alkawarin cewa za su sa ido sosai don tabbatar da cewa an yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata don amfanin da aka nufa.