Zuba Jari a Zamfara: Gwamna Lawal Ya Jawo Hankalin 'Yan Kasar Turkiyya

top-news


Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu nasarar jawo hankalin wasu jiga-jigan masu zuba jari 'yan ƙasar Turkiyya don su zuba jarinsu a Zamfara.

A ziyarar da ya kai ƙasar Turkiyya a farkon watan Yuli, Gwamna Lawal ya gana da masu zuba jari, tare da ziyartar wurare daban-daban. Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu yau a Gusau cewa, Gwamna Lawal ya fara wannan ziyarar aiki a ranar Lahadi, 30 ga watan Yuni, inda ya kwashe kwana shida a can.

Sanarwar ta bayyana cewa, gwamnan da tawagarsa sun ziyarci wurare da dama, ciki har da wuraren kayan amfanin gona na zamani, wurin samar da nonon shanu, kiwon kaji da kamfanin ƙera motocin noma (Tarakta) na Turk Traktor.

“A wannan ziyarar aiki, Gwamna Lawal ya fara ne da ziyartar Bursa City, inda kamfanin Direkci Group ke da wurin kayan amfanin gona na zamani mafi girma a ƙasar. Shugaban kamfanin, Mehmet Nurullah Direkçi, ya zagaya da gwamnan cikin wannan katafaren wuri.

“Kamfanin Direkci Group yana samar da harkokin noma ga ƙasar Turkiyya da sauran masu zuba jari ta hanyar kayan amfanin gona na zamani. Kamfanin zai samar da irin wannan shirin a jihar Zamfara.

“Idan kamfanin Direkci Group ya shigo Zamfara, zai samar da kayan amfanin gona na zamani kala-kala, ciki har da noman zamani mara iri, noman zamani mai iri, dashen shuka, da noman ayaba na zamani,” in ji sanarwar.

Yayin da yake a birnin Gaziantep, Gwamna Lawal ya ziyarci gonar noman madara ta Innova Dairy, wacce ke ba da shawarwari da sabbin hanyoyin kafawa da sarrafa gonakin zamani yadda ya kamata.

“Gonar Innova Dairy za ta kafa tsari a Jihar Zamfara don amfani da duk fasahohin zamani da suka haɗa da kiwon shanu na zamani, tsarin kula da garken dabbobi, tatsar madarar shanu, sarrafa taki da kayan aikin gona.”
NNPC Advert