Kungiyar Tsaffin Daliban Jami'ar Al-Qalam Ta Karrama Kwamandan Hisbah Na Katsina
- Katsina City News
- 08 Jul, 2024
- 294
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Lahadi, 7 ga watan Yuli, Kungiyar Tsaffin Daliban Jami'ar Musulunci ta Al-Qalam (Al-Qalam University Katsina Alumni Association) ta karrama Sheikh Aminu Usman (Abu Ammar), PhD, Kwamandan Hisbah na jihar Katsina, tare da Dr. Armaya'u Umar Zango, DVC Academics na Jami'ar Al-Qalam.
Taron bikin karramawar ya samu halartar manyan baki ciki har da Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, PhD; Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin jihar, Alhaji Jabiru Muhammad Tsauri; da Shugaban Jami'ar Al-Qalam, Farfesa Nasir Musa Yauri. Sauran mahalarta sun hada da malaman jami'o'i da tsoffin daliban da aka karrama.
Gwamnan jihar Katsina ya yaba da irin nazarin da kungiyar ta yi wajen zaɓen waɗanda za a karrama. Ya ce, "Na ji daɗi matuƙa da zuwana wannan waje domin hakan ya ba ni damar ƙarin sanin Dr. Armaya'u Umar Zango da irin ƙwazonsa. Nan gaba ba za mu je kala a wani waje ba." Gwamnan ya kuma bayyana Dr. Aminu Usman a matsayin matashi mai ƙwazo, inda ya ce, "Na san Dr. Aminu Usman tun tuni ba yau ba, kuma na san irin ƙoƙarinsa wajen kawo gyara a cikin al’umma. Wannan ne ma yasa muka kafa hukumar Hisbah ta jihar Katsina kuma muka bashi jagoranci saboda yana da kishin abin."
An gudanar da taron a dakin taro na M.A Digital da ke kan titin zuwa sakatariyar gwamnatin jihar Katsina, daga gidajen Barhim, da misalin karfe 9 na dare. Taron ya kasance cike da addu’o’i da fatan alheri daga iyalai, ‘yan’uwa, da abokan arziki na waɗanda suka samu karramawar.