Hukumar Hisbah a Katsina Ta Karɓi Gudunmawar Babura Daga Shugaban Karamar Hukumar Kaita
- Katsina City News
- 03 Jul, 2024
- 557
A ranar Talata, 2 ga watan July, Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta karɓi gudunmawar babura guda uku daga Shugaban Karamar Hukumar Kaita, Injiniya Bello Lawal 'Yandaki. Gudunmawar ta gudana ne a wani taron bada tallafi na kayan Baburan hawa da kayan wasanni da aka yi a sakatariyar Karamar Hukumar Kaita.
Da yake jawabi yayin taron, Injiniya 'Yandaki ya bayyana cewa wannan gudunmawa zai taimaka wajen yaki da munanan dabi'u da hukumar ta sa a gaba. Ya ce an yi hakan ne domin tallafawa aikin hukumar Hisbah wajen inganta tarbiyya da ɗa'a a tsakanin al’umma.
A nasa jawabin, Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Katsina, Sheikh Dakta Aminu Usman Abu Ammar, ya nuna matuƙar farin ciki da godiya ga Shugaban Karamar Hukumar Kaita da gwamnatin Jihar Katsina bisa wannan muhimmiyar gudunmawa. Sheikh Abu Ammar ya ce hukumar za ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro da shugabannin kananan hukumomi 34 a fadin jihar Katsina don tabbatar da kawo gyara da kuma shigar da matasa maza da mata a hanya mai kyau.
Babura uku, shugaban na ƙaramar hukumar Kaita ya bawa hukumar Hisbah ta hannun Babban Kwamanda Dakta Abu Ammar, shi kuma ya miƙa su ga shugaban Hisbah na ƙaramar hukumar Kaita.
Sheikh Aminu Usman ya jaddada cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da samar da zaman lafiya da inganta tarbiyya a jihar Katsina. Ya kuma godewa gwamnatin jihar bisa cikakken goyon baya da take ba hukumar Hisbah don tabbatar da nasara a ayyukansu.