Kula da Lafiya: Cututtukan da ake iya ɗaukarsu (Infectious Diseases)
- Katsina City News
- 01 Jul, 2024
- 545
Waɗannan cututtuka suna faruwa ne sakamakon harbuwa da ƙwayoyin cuta waɗanda ba a iya ganinsu da idanuwa sai an yi amfani da wata na'ura. Suna shiga jikin ɗan adam kai tsaye ko kuma ta hanyoyin mu'amala da wanda ke ɗauke da cutar, misali, yaro ko babba.
Alamomin Cututtuka da Yadda Suke Shiga Jikin Dan Adam
1. Alamomin Kamuwa da Cuta
Idan mutum ya kamu da cuta mai ɗaukarwa, za ka ga yana cikin zazzabi. Wannan cuta takan iya kama wanda ba ya ɗauke da ita, watau yana iya sa wa ɗan uwansa. Mafi yawanci, idan mutum ya kamu da wannan cuta sau ɗaya, ba zai sake kamuwa da irin ta ba har tsawon rayuwarsa. Misali, cutar kyanda.
2. Hanyoyin Shiga Jiki
Cutar tana iya shiga ta cikin duburar ɗan adam, ta hanyar shakar iska ta hanci ko baki, ko kuma ta hanyar fatar jiki musamman idan an samu rauni. Misalin ƙwayar cutar da ke shafar fatar jiki ita ce cutar tetanus, wadda aka fi ɗauka daga ƙasa da gurbataccen abu.
Misalan Hanyoyin da ake Kamawa da Cututtuka:
- Shan Gurɓataccen Ruwa ko Abinci: Ana iya kamuwa da cututtuka ta hanyar shan ruwa ko abinci da suka gurɓata.
- Shakar Iska: Ana iya kamuwa da cututtuka ta hanyar shakar gurɓatacciyar iska da ke ɗauke da ƙwayoyin cuta.
- Ta hanyar Kwari ko Dabbobi: Misali, namijin sauro na kawo zazzaɓi, kuma kare kan sa tangarda ga lafiyar ɗan adam idan ya ciji mutum.
- Tattaunawa da Masu Cuta: Ana iya ɗaukar cuta daga mutanen da ke ɗauke da ita, kamar zazzabin da ke shafar hanji, wanda ya yi katutu a Afirka.
A taƙaice, waɗannan su ne hanyoyin da ƙwayoyin cuta kan shiga cikin jikin ɗan adam su kawo masa illa. Wasu lokuta, cututtuka na haddasa rasa rayukan mutane maza da mata, yara da manya. Da fatan za mu kula da kyau, Allah kuma ya ba mu ikon kare jikunanmu domin hana su kamuwa da irin waɗannan cututtuka, Amin.
TUSHE: Littafin Kula da Lafiya na Safiya Yau'u Yamel