Rabani Da Batun Sakin Nnamdi Kanu - Hon. Tafoki

top-news

 
Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Kankara, Sabuwa, da Faskari, Hon. Ɗalhatu Shehu Tafoki, ya yi watsi da jita-jitan da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa yana da hannu wajen sakin tsohon ɗan tawaye Nnamdi Kanu.

Hon. Tafoki ya bayyana haka a taron manema labarai a Katsina, inda ya ce baya da alaƙa da takardar da ake cewa yana neman shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya saki Nnamdi Kanu.

A halin yanzu, wata takarda ta karade kafafen sada zumunta inda aka bayyana wasu 'yan majalisun tarayya su 46 wai sun sanya hannu a sakin Nnamdi Kanu. 

Hon. Tafoki ya ƙara da cewa bai san da wannan tafiya ba, kuma bai sanya hannu a takardar ba. Ya bayyana cewa idan ya sanya hannu, menene ribarsa, kuma yaushe ya sanya hannu? Ya ce wadanda suka samar da takardar ba za a iya gano su ba, don haka ya yi mamakin ganin sunansa a cikin jerin.

A cewarsa, shi ya fi amincewa da hadin kan ƙasa, kuma koda yaushe abin da yake yi kenan, domin ganin Najeriya ta ƙara dunkulewa.

Ya ce tun da Allah ya ba shi damar zama ɗan majalisar tarayya, yake ta fama da matsalar tsaro a yankin ƙananan hukumomin da yake wakilta domin ganin an shawo kan matsalar.

"Ban da aikin da ya wuce bin jami'an tsaro da hukumomin da suke da alaƙa da matsalar mutane na da suke fuskantar hare-hare a Faskari, Sabuwa, da Ƙanƙara," inji shi.

Ya ƙara da cewa yana ci gaba da ganawa da mutanen da bala'in 'yan bindiga ya shafa domin ba da tallafin da ake buƙata tare da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a yankin da yake wakilta.

Daga ƙarshe, Hon. Ɗalhatu Shehu Tafoki ya yi kira ga jama'ar da yake wakilta da sauran al'umma da su ci gaba da yi wa ƙasa addu'ar samun zaman lafiya.