Gwamna Radda Ya Karɓi Tawagar UNDP Don gudanar da Taron Tsaro
- Katsina City News
- 23 Jun, 2024
- 377
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya tarbi tawagar Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) a Filin Jirgin Saman Umaru Musa Yar'Adua da ke Katsina. Tawagar na karkashin jagorancin wakilin UNDP, Elsie Attafuah.
Wakilan UNDP sun ziyarci Katsina ne domin halartar taron tsaro na yankin Arewa maso Yamma, wanda za a gudanar a ranar Litinin, 26 ga Yuni, 2024. Wannan taro yana da nufin tattauna matsalolin tsaro da suka dade suna addabar yankin Arewa maso Yamma na Najeriya, ciki har da Jihar Katsina.
Ziyarar tawagar UNDP, karkashin jagorancin wakili Elsie Attafuah, tana nuna muhimmancin da al’ummar duniya ke bai wa kokarin magance matsalolin tsaro a yankin. Wannan taro yana zama wani muhimmin mataki na hadin gwiwa wajen magance matsalolin tsaro da yankin ke fuskanta.
Ta hanyar shirya wannan taro, ana sa ran samun hanyoyin warware matsalolin tsaro, ƙarfafa haɗin kai, da shimfiɗa hanyar zaman lafiya da ci gaba a Jihar Katsina da kuma yankin Arewa maso Yamma.