Yan Bindiga Sun Kashe Wanda Ya Kai Kudaden Fansa a Kaduna
- Katsina City News
- 20 Jun, 2024
- 477
Daga Abubakar Sadiq Isah
Yan bindiga sun kashe wani matashi mai shekaru 27 mai suna Abba a garin Jere, jihar Kaduna, bayan da ya kai naira miliyan 16 da babura guda uku don fansar wasu mutane tara da aka yi garkuwa da su. Abba, wanda ya shiga cikin tattaunawa da kai kudaden fansar, an harbe shi har lahira.
Shuaibu Hussaini, wani mazaunin yankin, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana cewa 'yan bindigar sun kai farmaki gidajen da ke Unguwar Iya a Jere a ranar 16 ga Afrilu, 2024, suka nemi naira miliyan 30. An kashe Abba ne a ranar Asabar da ta gabata bayan ya kai kudaden fansar da baburan.
Hussaini ya bayyana cewa daya daga cikin wadanda aka sako ya bayyana rashin jin dadin shugaban 'yan bindigar da Abba yayin tattaunawar, wanda hakan ya jawo kashe shi. Dangin Abba da suka yi kokarin gano shi sun samu umarnin daga 'yan bindigar su dauki gawarsa daga wani wurin da aka ayyana. Mutuwar Abba ta jefa al'umma cikin jimami, ya zuwa hada wannan rahoton hukumar 'yan sandan jihar Kaduna ba ta tabbatar da lamarin ba tukuna.