TATSUNIYA TA 29: Labarin Tsurondi
- Katsina City News
- 14 Jun, 2024
- 498
Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana wani Dodo ya rikida ya zama mutum, ya shiga wani gari neman aure. Da ya je mazaunin wasu mutane sai ya gaishe su. Ya sanar da su cewa shi bako ne, amma neman aure ne ya kawo shi garin. Ya kara yi musu bayani cewa ya fi son kyakkyawar mace, wadda babu kamar ita a garin.
Shi ke nan, sai mutanen nan suka yi masa kwatancen gidan wasu 'yan mata biyu, Awa da kanwarta Tsurondi. Da ya je gidan ya yi sallama, sai mai gidan ya fito suka gaisa. Daga nan bako ya yi wa mai gida bayanin abin da ya kawo shi. Sai uban 'yan matan ya ce: "To bari in turo su, duk wadda ta ce za ta aure ka sai in ba ka ita." Ya shiga cikin gida. Jim kadan sai Awa, watau babbar, ta fito. Da ya gan ta nan take ya ce yana son ta. Da ta gan shi kyakkyawa kuma bako ne sai ita ma ta yarda. Aka shirya biki, aka gama. Aka raka su bayan gari ita da mijinta za su tafi garin mijin.
Bayan ango da amarya sun kama hanya, sai kanwarta Tsurondi ta ce za ta raka ta. Amma sai Awa ta ce kada ta bi su. Kanwar ta yi juyin duniyar nan, amma Awa ta ki yarda. Sai Tsurondi ta zama kuda ta fada kan kayan amarya, suka kama hanya.
Can lokacin da suka isa dokar daji, sai iska ta dauke hular ango. Da matarsa Awa ta ga haka sai ta ce: "Mai gida hularka ta fadi." Sai ya ce da ita: "A nan na tsince ta da man." Suna cikin tafiya tana mamakin abin da mijinta ya ce, sai ta ga sandarsa ta fadi. Tana ganin haka, saboda son miji, sai ta ce da shi: "Mai gida sandarka ta fadi." Da mijin ya ji abin da ta ce sai ya ce da ita: "Ki bar ta, a nan na dauke ta." Ta yi shiru, suka ci gaba da tafiya. Da suka kara gaba kuma, sai babbar rigarsa ta zube a kasa. Awa ta kasa hakura, sai ta ce: "Mai gida ga rigarka ta sullube, ta fadi." Ita ma ya ce: "Bar ta, da mna a nan na dauke ta." Haka dai ya yi ta zubar da kayan jikinsa har ya zama tsirara. Sai kawai va zama wani dodo mai babban kaho a tsakiyar kansa da doguwar jela mai gasuka kowanne kamar girman adda.
Ganin haka ya sa Awa ta razana. Nan take ta barke da kuka, amma fa tana bin sa har suka isa gidansa. Bayan sun huta a gidan Dodo, kuma va fita shan iska, sai kanwarta ta rikida zuwa mutum. Da Awa ta gan ta, sai murna da mamaki suka kama ta, kuma ta dubi kanwar ta ce: "Tsurondi yaya aka yi kika biyo ni?" Sai ta ba ta labarin yadda ta yi. Shi ke nan kullum idan lokacin dawowar Dodo ya kusa, sai ta 6oye Kanwarta, kuma in gari ya waye, Dodo ya tafi farauta, sai ta fitar da kanwar. Haka dai suka yi ta fama har Awa ta sami ciki. Da lokacin haihuwa ya kusa, sai ta ce da kanwar ta kama hanya ta je gida ta gaya musu za ta zo haihuwa, amma kuma idan sun isa, a yi dabarar da za a kashe Dodon. A haka suka yi ban kwana.
Tsurondi ta zama tsuntsuwa ta tashi sama fir, sai garinsu. Tana isa gida ta ba mutanen gari labarin abin da Awa ta aura. Da suka ji haka, sai suka fara shirin kashe Dodo. Suka tona rami a dakin mahaifiyar Awa, a daidai inda Dodo zai zauna ranar suna.
Da watan haihuwar Awa ya kama, sai ta gaya wa Dodo za ta je gida domin ta haihu a cikin 'yan'uwanta. Mijin kuwa ya ba ta izini, har ma ya sa ta a hanya, ta isa gida lafiya. Bayan 'yan makwanni da isarta gida, sai ta haihu, kuma aka aika masa ya zo ya ga dansa. Sai ya yi murna, kuma ya sa ranar zuwansa. A ranar da Dodo zai isa tun da safe iyayen Awa suka hura wuta a ramin da suka tona. Suka jefa manyan guma-gumai, wuta ta hadu sosai. Daga nan suka dora gadon kara a kan ramin, sannan aka shimfida tabarma a kai. Da Dodo ya zo, aka zaunar da shi a kan tabarmar, aka kuma mika masa dansa domin ya gani. Can sai ya fara ji kamar ana muntsinar sa a duwaiwai, bai san ramin wuta ne a karkashinsa ba. Da wuta ta ci karan, sai suka burma shi da dansa. Nan dai ya yi kici-kicin jefo dan waje, amma aka sake mayar masa shi, har dai suka kone kurmus a cikin ramin nan.
Haka na faruwa, sai mutanen gidan suka tashi daga wannan gidan suka koma wani sabo da suka gina. Bayan wasu 'yan shekaru sai kurna da kanya suka tsiro a inda Dodo da đansa suka kone. Gasu kuwa da zuba 'ya' ya masu yawa da kyau ko da a ido. Amma sai mutanen garin suka hana kowa ci saboda tsoron abin da zai iya biyowa baya. Duk shekara sai dai 'ya'yan su rube babu mai ci.
Ana nan, ana zaune a haka wata rana daya daga cikin matan Sarki ta fita yawon shakatawa, kuma tana da ciki sai ta hango kanyar nan da kurnar. Sha'awa ta sa ta debi kanya da kurna ta sha, ta kuma zuba wasu a cikin kwaryarta. Da ta gama ta kama hanya ta fara tafiya, sai bishiyoyin nan biyu suka fara bin ta suna waka suna cewa:
Lokacin da nake mutum ba a so ni ba,
Da na zama kanya za a sha ni,
Kurna karama, Kanya babba.
Haka suka yi ta bin ta. Idan ta juya ta yi musu magana, sai ta zubar da kurna da kanyar da ke cikin kwaryar, to amma ba su daina bin ta ba. Da ta zo za ta shiga gidan Sarki, da dogarai suka ga abin da take tafe da shi, sai suka hana ta shiga, suka kore ta; sai ta je wajen wasu mutane tana kuka. Da suka tambaye ta abin da ya sa take kuka, sai ta yi musu bayani. Daga nan kuma ta nemi taimakonsu. Mutanen suka ce za su iya taimaka mata, to amma ta fara yi musu bayani dalla-dalla. Kafin ma ta fara bayanin, sai ga bishiyoyin nan sun biyo ta suna waka. Nan da nan mutanen suka kore ta, suka ce wannan abu yafi karfinsu. Ta ci gaba da tafiya a dajin nan, can sai ta hadu da wasu tsuntsaye suna hira. Za ta wuce, sai tsuntsayen suka tambaye ta abin da ya same ta. Ta ce, ai ba za su iya taimaka mata ba, tun da mutane ma sun kasa taimakonta, su bar ta kawai ta je ta mutu. Sai tsuntsaye suka kafe ta gaya musu ko me ke damun ta. Da ta ga dai lallai sun matsa, sai ta kwashe labarin abin da ya dame ta ta gaya musu. Kafin ma a gama fada musu sai ga bishiyoyin tunkaro su, suna tafe suna waka. Sun ganin haka sai kawai babbar cikin tsuntsayen ta ce, duk tsuntsayen da ke nan su fada wa bishiyoyin nan su cinye ganyensu, kada su bar ko da ganye daya. Tsuntsayen nan kuwa suna da dimbin yawa, kuma wasu daga cikinsu da man suna jin yunwa. Nan take suka yi dango a kan bishiyoyin nan har suka cinye ganyensu gaba daya.
Ganin tsuntsaye sun cinye ganyen bishiyoyin, sai matar Sarki ta yi godiya. Da tsuntsayen suka ga halin da take ciki na goyon tsohon ciki, sai suka tambaye ta ko za ta iya zuwa gida, sai ta ce za ta iya. Ta kama hanyar gida. Ba ta yi tafiya mai yawa ba, sai ga dogarai, Sarki ya sa su nemo masa mata duk inda ta shiga. Da dogarai suka gan ta, sai murna ta kama su. Nan da nan suka dora ta a kan dokin da suka je da shi. Ayarinta ya motsa, jim kadan suka shiga gari. Da jama'a suka ji ta dawo, sai suka kama murna.
Bayan 'yan kwanaki sai matar Sarki ta haifi da namiji. Saboda labarin da ta bayar na irin taimakon da tsuntsaye suka yi mata, sai aka sa wa yaron suna Yarima Mai Tsuntsaye. Kurunkus.
TUSHE: Mun ciro wannan labarin daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI Na Dakta Bukar Usman