INA RUBUTA LITTAFIN DARASIN RAYUWA TA -Malam Garba Shehu,
- Katsina City News
- 10 Jun, 2024
- 353
Tsohon Kakakin Shugaban Kasa Buhari
Daga Danjuma Katsina
@ Katsina Times
Malam Garba Shehu, tsohon kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa jaridun Katsina Times cewa, yanzu yana more hutun sa da aikin rubuta wani littafi na darasin rayuwa a aikin sa, wanda zai taimaka wa matasa da kuma ɗaliban aikin jarida.
Ya bayyana haka ne a wata hira da babban Editan jaridun Katsina Times, Muhammad Danjuma ya yi da shi a Kano a kwanakin baya, wanda tana daga cikin cikakkiyar hirarsa ta farko da ya yi bayan sun bar fadar shugaban kasa.
Malam Garba ya ce, tun da ya fara aikin gwamnati zuwa lokacin aiki da 'yan siyasa duk yana adana muhimman bayanan darasin da ya samu.
Ya ce yanzu da ya ajiye aiki, bayan gwamnatinsu ta ƙare ya tattaro duk waɗannan bayanan yana rubuta littafin da zai zama kamar taskace tarihi.
Ya ce littafin kuma zai zama fitila ga 'yan jarida, matasa da ɗalibai masu koyon aikin jarida da ma waɗanda suke son shiga aikin.
Malam Garba Shehu ya ce, aikin rubutun ya kusa kammala a lokacin da muka yi hirar da shi.
Ya ce wata ƙila ya yi taron gabatar da littafin ga al'umma, ko kuma ya sake shi ga duniya a karanta.
Malam Garba Shehu ya ce, har yanzu yana tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya misalata da mutumin kirki da za a daɗe ƙasar nan ba ta ga irin sa ba.
Ya ce duk safiya sai ya sayi jaridu daga Kano an kai masa har gidansa da ke Daura jihar Katsina.
"Duk jaridun da ke fitowa ni nake haɗa su in sa a mota a kai masa har Daura kullum rana. Kuma yana karantawa," in ji shi.
Malam Garba Shehu ya ce; "Nakan je Daura duk lokacin da buƙatar haka ta taso."
Ko waya ka rage bugawa? Tambayar da muka yi masa ke nan. "Wannan gaskiya ne. Don ka san wancan ofis ne na gwamnati dole waya ta yi ta bugawa. Yanzu kuma ina hutawa sai wayar iyali abokai da kuma aminai da 'yan'uwa."
Cikakkiyar hirar za mu dora ta a shafinmu na Katsina Times TV da ke kan You Tube da sauran shafukan Katsina Times da ke www.katsinatimes.com.