KARFIN MU NE YA KARE MUKE ROKON GWAMNATI TA SHIGO- Mazauna Unguwannin Sabuwar Dutsin Safe Low-cost da Malali.
- Katsina City News
- 09 Jun, 2024
- 603
A cigaba da ROKON da suke wa Gwamnatin Jihar Katsina na ta kawo musu dauki dangane da wata babbar hanyar ruwa da ke cigaba da lakume masu gidaje, al'ummar Sabuwar Dustin safe low cost da malali sun yi Karin haske dangane da Lamarin inda suka bayyana cewa da taimakon wasu masu hali a yankin, tare da aikin gayya sun kashe makudan kudade wajen takaita Al'amarin inda suka bayyana cewa ko a Yan satuttukan da suka gabata sun kashe irin wadannan kudade wajen canja ma Ruwan hanya tare da rage masa karfin barnan da ya ka iya yi.
Lura da hadarin da mazaunan suke na fuskanta na amabaliyar Ruwa.
Mai Unguwar malali, Alh Mustapha Abubakar yayi Karin haske a lokacinda yake magana da yan jarida, bayan duba wasu ayyukan gayya da mazauna wannan yanki suka gudanar a dai-dai karfinsu.
Mai unguwa Mustapha Abubakar ya bayyana cewa, wannan unguwa tana dauke da al'ummar masu yawa wadanda koda yaushe suke biyayya ga duk wasu kudurori da tsare-tsaren gwamnati, yana mai cewa babbar matsalar wannan yanki itace rashin hanyoyin ruwa da take haifar da ambaliya da zaizayewar gidaje musamman a lokutan Damina.
Mai Unguwar Wanda ya bayyana jindadinsa da yabawa ayyukan gayya da hadin kai na mazauna wannan yanki, yayi roko ga gwamnatin jihar Katsina data kawo dauki na gaggawa ga wannan al'ummar domin cetosu daga wannan Matsala, wadda a cewarsa abin yakai saidai ace "Innalillahi....."
Ya kara da cewa, wadannan al'ummar sunyi aikin gyaran hanyoyin ruwa gwargwadon karfin su, amma akasarin aikin saidai gwamnati, Daganan sai yayi addu'ar qarin zaman lafiya da yalwar arziki ga jihar Katsina da kasa baki daya.
Za'a iya tunawa dai al'ummar unguwannin Sabuwar Dutsin Safe da bayan gidan Taki ya zuwa malali sun jima suna fama da matsalar ambaliar ruwa da zaizayar kasa musamman lokutan damina a sakamakon rashin wadatattun hanyoyin ruwa a wadannan unguwannin.
A domin hakane, suke kara roko ga gwamnatin adalin gwamna mal Dikko Radda akan takai musu dauki na gaggawa kasancewar Damina ta fara kankama.