Tsohuwar 'Yar Majalisar Tarayya Ta Koka Kan Rashin Biyan su Haƙƙoƙin su na Tsawon Shekaru
- Katsina City News
- 05 Jun, 2024
- 564
Muhammad Ali Hafizy, Katsina Times
Hajiya Mariya Abdullahi Bakori, tsohuwar 'yar majalisar tarayya a Najeriya a shekarar 1991, ta bayyana irin kalubalen da suka fuskanta yayin zamansu a majalisa, a wata tattaunawa da jaridar Katsina Times da Taskar Labarai suka yi da ita.
A cewar Hajiya Mariya, lokacin da aka zaɓe su a matsayin 'yan majalisar tarayya, zaɓen ya kasance na gaskiya da rikon amana. Ta ce, "Zaɓen da aka yi mana, an yi shi tsakani da Allah, kuma duniya ta shaida cewa ba a taɓa yin sahihin zaɓe irin wannan ba."
Ta kara da cewa bayan zaɓen su, an fara da zagayawa cikin Jihohin Nijeriya domin sanin halin da ƙasa take ciki da kuma yadda za su tsara dokoki idan sun shiga majalisar. Duk da haka, sojoji sun yi masu dirar mikiya a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Janar Sani Abacha, inda suka kora su zuwa garuruwansu ba tare da ba su haƙƙoƙinsu ba.
Hajiya Mariya ta bayyana cewa tun daga lokacin, sun yi ta fafutukar ganin an biya su haƙƙoƙinsu na albashi da ayyukan da suka yi, amma hakan ya ci tura. Har ma wani daga cikin su an ɗaure shi saboda neman haƙƙin su, kuma an ɓoye fayilolin su domin hana su haƙƙoƙinsu.
Ta ce shugaban ƙasa na yanzu, Bola Ahmed Tinubu, wanda shima yana cikin majalisar dattawa a wancan lokacin, yana cikin waɗanda abin ya shafa. Saboda haka, suna roƙon shugaban ƙasa ya yi masu jagora wajen tabbatar da haƙƙoƙinsu waɗanda aka hana su tsawon shekaru, tun da shi ma yasan abubuwan da suka faru a lokacin.
Zaku iya samun cikakken bayanin tattaunawar ta bidiyo a shafukan jaridun Katsina Times da Taskar Labarai.