ILMI TSANI NE ..INJI GWAMNAN ZAMFARA
- Katsina City News
- 26 May, 2024
- 458
@ Katsina Times
Gwamanan jihar Zamfara Dauda Lawal ya bayyana ilimi a matsayin wani tsani, matakala ta kaiwa ga samun duk wani abin nema a duniyar nan.
Gwamnan ya halarci taron yaye ɗalibai karo na uku da na huɗu na Jami'ar tarayya, wanda ya gudana a filin taro na Jami'ar da ke Gusau a jiya Asabar.
Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar yau a Gusau cewa, Gwamna Lawal ya shelanta bayar da gurbin karatu ga duk wanda ya zo na ɗaya a Jami'ar.
Cikin jawabin sa a wurin taron, Gwamnan ya yaba wa shugabannin Jami'ar game da yadda suka iya ririta ɗan abin da suke da shi, duk da ɗimbin ƙalubalen da suke fuskanta.
Ya ce, "Ina matuƙar farin cikin kasancewa da ku yau a wannan bikin yaye ɗalibai karo na uku da na huɗu a wannan jajirtacciyar Jami'a, Jami'ar gwamnatin tarayya ta Gusau. Ina taya jami'ar nan murnar samun wannan nasara, duk kuwa da matsalolin da suke fuskanta tun lokacin da aka kafa ta. Ina kuma yaba wa iyaye da ɗalibai bisa sadaukarwar da suka nuna har zuwa wannan matsayi.
Muna sa ran samun makoma mai kyau kuma mai albarka duk da tarin ƙalubalen da muke fuskanta a matsayinmu na jiha kuma al'umma. Muna yin addu'a kuma muna aiki ba dare ba rana don samar da makoma mai kyau. Duk waɗannan matsaloli za su wuce da izinin Allah Maɗaukakin Sarki.”
Gwamnan ya yi ƙarin haske kan ƙoƙarin gwamnatinsa na gyara harkar ilimi a Jihar Zamfara bayan kafa dokar ta-ɓaci a bara.
“A matsayinmu na gwamnati, mun ƙuduri aniyar ilimantar da duk ’ya’yan Zamfara. Ilimi shi ne ginshiƙin da ke haskaka ruyuwar ɗan adam.
“Mun ware maƙudan kuɗaɗe ga ɓangaren ilimi a cikin kasafin kuɗinmu na 2024 kuma muna fatan za mu kai ga babban matsayi a 2025, 2026, da 2027. Muna fatan cimma kashi 25 zuwa 30 na haɓaka tsarin ilimi. Tare da samar da ingantaccen tsari a fannin da sarrafa albarkatun da ya ƙunsa, muna da ƙwarin gwiwar cewa za mu farfaɗo da ababen more rayuwa, ɗaukar ƙwararrun malamai, horarwa da sake horar da waɗanda ake da su.
“Za kuma mu ƙara yawan masu karatu a makarantun firamare da na gaba da firamare ta hanyar wayar da kan jama’a da samar da ingantattun wuraren koyo da koyarwa. Ilimi kyauta ne, kuma muna fatan ya zama wajibi ga kowa.
“Mun kuma yi wa manyan makarantunmu da ke jihar kason kuɗi mai yawa don fara aikin gyara su zuwa matakai masu inganci. A karon farko Jami’ar Jihar Zamfara na shirye-shiryen amincewa da shirin Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa. Mun umurci ’yan kwangilar da gwamnatin da ta shuɗe ta tilastawa barin wuraren aiki da su koma bakin aiki, kuma muna fatan nan da watanni masu zuwa, rukunin dindindin na jami’ar zai fara aiki. A lokaci guda, NUC za ta amince ga duk kwasa-kwasai.
“Mun karɓi mulki a jihar da gwamnati ta ƙi biyan kuɗaɗen jarrabawar WEAC da NECO har na biliyoyin Naira fiye da shekaru uku. Dole muka yi shiri na musamman da hukumomin, kuma tun daga lokacin an fara biyan kuɗi a kan kari kuma za a kammala su a kan lokaci.
“A cikin ƙarancin albarkatunmu, za mu ci gaba da bayar da taimako ga jami’a. Burinmu shi ne mu ƙara haɓaka ilimi a jiharmu ta yadda za a samu damarmaki ga ɗaukacin matasanmu da za a horar da su don kai ga ƙololuwar da ilimi ke samarwa.”