Labarin Sarki da Gizo; Tatsuniya ta (20) Ga ta nan. ga ta nanku.
- Katsina City News
- 23 May, 2024
- 573
An yi wata tsohuwa a wani dan kauye: tana da
marakinta kyakkyawan gaske; ga shi kosasshe.
Ana nan wata rana Gizo ya je gidan wannan tsohuwa bara sai wannan maraki. Sai ya fasa bara ya fita daga gidan, ya sheka a mi gidan Sarki. Ya fadi a gaban Sarkı, ya ce: "Ko kunnuwan Sarki nawa ne" Sarki ya ce: "Biyu.
Gizo Da Sarki Sai ya ce wa Sarki: "Kara biyu, a kan biyu ka sha labari"
Sarki ya ce: Na Rara." Sai Gizo ya ce: "Akwai wani kyakkawan sa a gidan wata tsohuwa. in
ba gidanka ba, to sai gidana."
Sai Sarki ya ce: "To shi ke nan. Sai Sarki ya tura dogarai don a kamo kuma a kawo masa wannan san.
Da dogarai suka kama hanya ba su tsaya a ko'ina ba sai a gidan tsohuwa.
Suka same ta, suka isar da sakon Sarki.
Da ta ji bayanin dogaran Sarki sai ta ce: "To yaya zan yi yau.
Tafi tafiye tirke, Dalilin tsohuwa na fadin haka shi ne wannan sa ba ya yin komai sai da
izninta. Dogaran Sarki suka yi, suka yi su kwance sa daga turkensa su tan da shi amma abin ya gagara. Can dai sai tsohuwa ta saka san a gaba tana masa waka tana cewa:
Sarakan bana kwadayi gare su,
Abu kadan a kai ka fada,
Abu kadan a kai ka fada,
Har gaban Sarki."
Haka ta rinka rera wannan waka san yana yi mata biyayya har , gidan Sarki.
Da suka isa fada Sarki ya ga sa sai ya ce za a yanka shi. Sai ya tambayi tsohuwa abin da take so daga jikin san. Sai ta ce ita abin da take so
ne kayan ciki. Sarki ya ba da umarni aka yanka sa, aka fede aka debi kayan ciki aka ba tsohuwa.
Da tsohuwa ta koma gidanta sai ta shanya kayan cikin nan, ta mai da hankalinta a kan aikinta na gona. Wata rana ta dawo daga gona sai ta to an yi mata shara a gida da sauran aikace-aikacen gida. Sai abin ya ba ta mamaki tana tunanin ba ta da kowa, kuma wane ne zai zo ya yi mata wannan aiki. Kashe-gari ma aka sake yi mata aikin.
Ashe da ma kayan cikin nan da tsohuwa ta shanya su ke rikida su koma kyawawa guda biyar. Kullum idan ta tafi gona, sai su fito daga
karkashin gadonta inda suke kwana su yi mata hidima.
Wata rana sai tsohuwa ta ce tun da ba ta san mai taimaka mata ba, za ta shirya kamar za ta gona sai ta buya a bayan danga domin ta ga mai yi mata wannan hidima. Haka kuwa aka yi. Ta 6uya a bayan danga, can sai ga 'yan mata kyawawa sun fito daga karkashin gadonta. Nan da nan suka fara aikace-aikacen gida, suka bude randunanta suka cika da ruwa, suka
yi share-share da duk sauran ayyukan da suka kamata. Can sai kwatsam tsohuwa ta fado tsakar gida suka gan ta. Ta yi musu magana.
Daga wannan rana sai 'yan matan nan suka daina buya, suka zauna da tsohuwa suna taya ta aikace-aikacen gida. Bayan wasu 'yan kwanaki sai ta sa wa kowacce budurwa suna. Akwai Ta-kitse da Ta-hanji da Ta-tumbi da Ta-hanta da Ta-huhu. kawai shi Ana nan, ana nan wata rana Gizo ya sake komawa bara gidan tsohuwa, sai ya hango wadannan "yan mata kyawawa a gidan tsohuwa. Ya fita a gudu sai gidan Sarki. Da ya isa sai ya ce: "Sarki, Sarki kunnenka nawa?
Sai Sarki ya ce: "Biyu."
Sai Gizo ya ce: "Ka kara biyu ka sha labari." Sai Sarki ya ce: Na kara.
Daga nan sai Gizo ya kwashe labarin 'yan matan da ya gani ya gayawa Sarki.
Nan take sai Sarki ya tura fadawa a kawo masa guda daya daga cikinsu.
Sai dogarai suka je gidan tsohuwa suka yi sallama da ita. Da ta fito sai ta ga fadawan Sarki ne. Sai ta koma gida ta fara waka tana cewa: Ta-hanta, Ta-hanta, Debo ruwa ki kai wa bakon da ke waje," Sai Ta-hanta ta ce:Tabdi, in debo ruwa Ta-huhu tana nan." Sai tsohuwa ta sake rera waka ta ce: Ta-huhu, Ta-huhu,
Debo ruwa ki kai wa bakon da ke waje."
Sai ta ce: Tabdi, in debo ruwa in kai wa bakon da ke waje, ga Ta-hanji
tana nan ?"
Da haka, da haka har tsohuwa ta gama zagaya 'yan matan nan, har ta kai kan Ta-kitse. Ita ce ta karshe. Sai ta dauko koko, ta debi ruwa ta kai
wa bakon da ke waje. Tana fita da ruwan nan sai fadawa suka kama ta, sai gaban Sarki.
Da Sarki ya gan ta sai ya ce zai aure ta. Nan da nan kuwa ya aure ta ya sa ta cikin matansa.
Amma ba ta fita rana, kuma ba ta zuwa kusa da wuta domin ita kitse ce, idan ta sha rana ko zafin wuta ya buge ta sai ta narke.
Wata rana Sarki ya tafi yaki, sai kishiyoyin Ta-kitse suka ce sai ta fito
ta yi girki, tun da ita ma auro ta aka yi kamar su.
Da suka matsanta sai ta yi girki, sai ta je bakin murhu. Tana zuwa sai ta narke. Da tsuntsun Sarki ya ga abin da ya faru sai ya yi tsalle ya tashi sai filin daga inda su Sarki suke fafatawa da abokan gaba. Sai tsuntsun nan ya
fara waka yana cewa:
"Sarki, Sarki,
Ka mai da yaki baya,
Ta-kitse ta narke,
Ta narke ta zama ruwa.
Da Sarki ya ji wakar tsuntsun nan sai ya bar yaki ya komo gida.
Sai ya tarar har Ta-kitse ta gama narkewa.
Saboda laifin da matansa suka yi masa na sa Ta-kitse girki a kan dole, sai ya kore su gaba daya ya yi zamansa shi kadai.
Kurunkus.
Mun ciro wannan Labarin daga littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman