YAUDARA DA RAƊAƊIN TSADAR RAYUWA A MULKIN TINUBU
- Katsina City News
- 22 May, 2024
- 699
Daga: Farfesa Usman Yusuf
22, Mayu, 2024
A shekara ɗaya ta farkon mulkin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya jefa 'yan Najeriya cikin matsanancin raɗaɗin tsadar rayuwar da suka koma faƙirai da mabarata a cikin ƙasar su.
Babban abin takaici ne matuƙa ganin irin yadda 'yan Najeriya, musamman mata da ƙananan yara ke fuskantar ƙasƙancin bin dogon layi, su na karɓar tallafin kofin shinkafa, kamar irin yadda ke faruwa a Sudan da Zirin Gaza, inda yaƙi ya ragargaza yankunan su.
Hakan fa na faruwa a ƙasar nan a halin da mu ba yaƙin ne ya haddasa mana wannan ƙuncin rayuwa ba, kuma ba ƙarancin ruwan sama ko fari ne aka fuskanta ba.
Kawai dai wannan raɗaɗin tsadar rayuwa da mawuyacin halin da ake fama da shi, sun faru ne sakamakon yadda Shugaba Tinubu ya tattago tsare-tsaren tattalin arziki wanda Bankin Duniya ya rattaba masa, wato cire tallafin fetur, karya darajar Naira, ƙarin kuɗin ruwa da ƙarin kuɗin wutar lantarki.
Waɗannan gurɓatattun tsare-tsare sun haifar da gagarimin hauhawar farashi, wanda ya cilla malejin tsadar rayuwa sama, wanda tsawon shekaru 28 kenan ba a fuskanci irin wannan tarangahuma ba. Malejin tsadar rayuwa ya cilla sama da kashi 33% bisa 100%, yayin da malejin hauhawar farashin kayan abinci da kayan masarufi ya dangwali kashi 40% bisa 100%.
A Najeriya, ƙasar da a yanzu mutum miliyan 133 (wato kashi 65% na 'yan ƙasa) suka rufta cikin kwazazzabon ƙangin talauci, sannan fiye da yara miliyan 20 na gararamba kan titina, ba su zuwa makaranta, waɗannan gigitattun tsare-tsaren da Tinubu ya bijiro da su, ba su amfana komai ba, sai ƙara jefa miliyoyin jama'a cikin fatara da talauci, sai ƙara ambaliyar yara kan titina, waɗanda raɗaɗin tsadar rayuwa ta sa iyaye ba su iya biya wa 'ya'yan su kuɗin makaranta.
A halin yanzu miliyoyin 'yan Najeriya, musamman mata da ƙananan yara na kwantawa ba su ci komai ba, kuma ba su da tabbacin samun abin da za su ci idan gari ya waye masu.
Magidanta da dama na gudu su tsallake iyalin su, su bar matan su da ƙananan yara, saboda ba su iya ciyar da iyalan su.
Tallafin ci-ka-mutu
Abin haushi, takaici da tausayi shi ne, gwamnati ba ta da wata hanyar magance wannan gagarimar matsalar da ta ƙaƙaba wa jama'a, sai raba wa marasa galihu tallafin abincin da Bahaushe ke kira 'ci-ka-mutu'.
A ranar 8 ga watan Fabrairun 2024, Shugaba Tinubu ya umarci a raba metrik tan 42,000 na kayan abinci daga rumbun Gwamantin Tarayya, wanda ya ce a raba kyauta ga marasa galihu. To yanzu dai watanni 4 kenan, amma marasa galihu ba su samu komai ba.
Maganar gaskiya ita ce, gwamnatin tarayya yaudarar mutane ta ke yi, saboda ta san babu komai cikin rumbunan ta. Wani gwamnan wata jiha a Arewa da aka shigar cikin wannan ƙarambosuwa, har hutun kwanaki 5 ya bayar, wai domin jama'a su fita su samu damar karɓar tallafin abincin da ya san babu shi, babu alamar sa.
Abin takaici ne matuƙa, ganin cewa yau shekaru 64 bayan samun 'yanci, har yanzu shugabanni na maida 'yan Najeriya mabarata.
Barazana Ga Harkar Ilimi
Ilmin yara bai taɓa lalacewa da taɓarɓarewa ba kamar yanzu, saboda irin yadda ‘yan ta'adda ke kutsawa cikin makarantu suna yin lodi da jidar ɗalibai. Shekaru 10 bayan kwasar dalibai mata 276 daga Chibok Jihar Borno, 'yan ta'adda sun sake jidar ɗalibai a Gusau Jihar Zamfara, Dutsinma Jihar Katsina, Gada Jihar Sokoto, Kuriga Jihar Kaduna da Ekiti, duk a cikin watanni 8 na farkon mulkin Tinubu.
Duk da irin wannan lodi da jidar ɗalibai da mahara ke ci gaba da yi, har yanzu babu wata gwamnatin jiha ko ta tarayya da ke yin wani hoɓɓasa domin samar da tsaro a waɗannan makarantu, saboda 'ya'yan talakawa ne kaɗai ke fuskantar barazana a cikin makarantun.
Taɓarɓarewar Tsarin Kiwon Lafiya
Tsarin kiwon lafiya a Najeriya ya taɓarɓare, lalacewar wasu ɗakunan kwantar da marasa lafiya ya yi munin da a wasu asibitocin ma kai kamar mayankar dabbobi ce. An yi watsi da Cibiyoyin Kula da Lafiya a Matakin Farko (PHC). Wato 'yan gidoga da gadangarƙama sun ƙwace tsarin kuɗaɗe na kiwon lafiya, da sunan HMO, sun bar marasa lafiya da jami'an kiwon lafiya cikin jangwangwama.
Ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi kwanan nan babbar barazana ce sosai ga ɗorewar kiwon lafiya a Najeriya. Asibitoci da yawa ba za su iya biyan kuɗin wutar lantarki ba. Ga hujja nan mun gani a bidiyon wani Likita da aka watsa, wanda aka nuno yana kukan an kawo masa 'bil' na kuɗin wuta, zai biya Naira miliyan 25.3.
Jami'an kula da lafiya sai ci gaba da ficewa suke yi daga Najeriya, su na tururuwa zuwa wasu ƙasashe, saboda rashin nagartaccen tsarin kula da lafiya a Najeriya. Babu nagartattun asibitoci masu inganci, babu kayan aiki masu inganci, sai rashin biyan albashi wadatacce.
Wani rahoton baya-bayan nan da Hukumar Kula da Likitocin Najeriya ta wallafa, ya tabbatar da cewa akwai likitoci 130,000 masu rajista a Najeriya. Su ne ke kula da mutum miliyan 200, lamarin da ke nufin duk likita 1 na kula da marasa lafiya mutum 1,500 kenan.
Ita kuwa Hukumar Kula da Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WHO), ta ƙayyade duk likita 1 ya kamata yana kula da marar lafiya 600 ne. Hakan ya nuna irin babban ƙalubalen da ake fuskanta a fannin kula da lafiya.
Miliyoyin 'yan Najeriya a yanzu ba su iya sayen magunguna, sun ma daina amfani da magungunan, saboda ba su da sukunin iya sayen magani. Hakan ya sa sun rungumi magungunan gargajiya, wanda hakan ya haifar da ƙaruwar cututtuka da mace-mace. Wasu kuma sun rungumi yi wa marasa lafiya addu'o'in neman samun sauƙi.
Ƙididdigar alƙaluman bayanai daga Ƙungiyar Likitochin da ke kula da masu chiwon hawan jini (Nigerian Hypertension Society'), sun tabbatar da cewa daga cikin 'yan Najeriya mutum miliyan 70 masu fama da ciwon hawan jini, rabin su, wato mutum miliyan 35 ba su shan magani, saboda kawai tsadar da magungunan suka yi. Hakan ya sa likitoci sai ƙara samun ambaliyar masu fama da ciwon hawan-jini ake ta yi masu zuwa ganin likita da cututtuka irin su shanyewar ɓarin jiki, ciwon ƙoda, ciwon zuciya da yawan mace-mace.
Cikin shekarar da ta gabata, asibitocin Najeriya sun sha fama da yawaitar kwantar da ƙananan yara masu fama da cututtukan tsananin yunwa wanda ake kira ‘Marasmus’ da 'Kwashiokor.'
Ƙananan yara 'ya'yan talakawa na ci gaba da mutawa cututtukan da alluran riga-kafi za su iya daƙile su, kamar baƙon-dauro, amai da gudawa, limoniya da sanƙarau, saboda rashin samun kulawa daga fannin kiwon lafiya.
Taɓarɓarewar Tsaro a Najeriya
Saɓanin farfagandar samun ci gaba da gwamnati ta riƙa yi, da kuma rufa-rufa dangane da matsalar tsaro, maganar gaskiyar halin da ake ciki musamman a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, babu wani ci gaba. Har yanzu 'yan bindiga na mamaye da yankuna masu yawa da faɗi a yankunan karkara, tsawon shekaru 15 na Boko Haram da shekaru 9 na 'yan bindiga.
Har yanzu ana ci gaba da zubar da jinin mutanen da ba su ji ba su gani ba, ana ci gaba da tarwatsa ƙauyuka, ana fatattakar mazauna ƙauyukan daga gidajen su, ko a yi garkuwa da su domin a karɓar kuɗin fansa.
Ana korar manoma daga gonakin su, ko a ƙaƙaba masu harajin tilas kan amfanin gonar su.
Har yanzu yawancin manyan titina hawan su kawai ake yi a cikin fargaba, domin 'yan ta'adda na ci gaba da tare hanya su na kwasar mutane, su kashe wasu, su kwashi wasu fasinjoji domin a biya fansa. Haka kashe-kashen rikicin ƙabilanci ko na addini na ci gaba, an kasa magancewa.
Gwamnati ta manta da mata 400 da ƙananan yara, waɗanda Boko Haram su ka kama daga Sansanin Masu Gudun Hijira a Gamboru Ngala, Jihar Barno. An kama su tun a ranar 3 ga Maris, 2024.
Shauƙi, zumuɗi da ƙarfin halin da sojojin mu ke da shi wajen tunkarar 'yan ta'adda, duk ya ragu, saboda yadda 'yan ta'adda ke ci gaba da yi masu kwanton-ɓauna su na kashe su a wasu sassan ƙasar nan.
Cikin watanni 8 da suka gabata, an kashe sojoji sama da 500, bisa la'akari da rahotannin da aka buga.
Gaggawar janye sojoji daga wasu yankuna biyu da 'yan bindiga suka mamaye a cikin Ƙaramar Hukumar Maru chikin Jihar Zamfara da Ƙaramar Hukumar Shiroro cikin Jihar Neja, inda aka kashe sojoji, alamomi ne na rashin jin daɗi da gajiyar fafata yaƙi a ɓangaren dakarun mu.
Zuwan Gwamnonin Arewa Amurka
Yayin da 'yan ta'adda da 'yan bindiga ke ci gaba da ragargazar Arewa, sai Gwamnonin Arewa 10 suka rangaɗa zuwa Amurka, domin neman mafita da hanyoyin magance matsalar tsaro a jihohin su. Na sha faɗa ba sau ɗaya ko sau biyu ba, cewa matsalar tsaron da ke addabar mu ta cikin gida ce, kuma tilas a cikin gida za a nemi magance ta, ba a Abuja ko New York ko Washington DC ko wani wuri can daban ba. Ƙungiyoyin 'yan sa-kai da wasu gwamnoni suka kafa a cikin jihar su, ba su tsinana komai ba, sai ma ƙara ruruta wutar zubar da jini kawai.
Babu sauran nuƙu-nuƙu, yanzu kowa ya san cewa gwamnatocin Amurka da Faransa na ta kamun-ƙafa ga Gwamnatin Tinubu, domin su kafa sansanonin sojojin su cikin Najeriya, bayan korar su da aka yi daga Mali, Nijar da Burkina Faso.
Babban abin damuwa shi ne a daidai wannan lokaci ne kuma gwamnonin Arewa 10 suka je Amurka, bisa wata gayyatar su da Cibiyar USIP ta yi. Wannan gayyata za ta iya kasancewa ta na da alaƙa ko nasaba da yunƙurin kafa sansanin sojojin Amurka a Najeriya.
Magance matsalolin tsaro a Najeriya na buƙatar tsari na gaskiya, kuma a yi wa matsalar sha-kundum, ta hanyar janyo waɗanda lamarin ya shafa, maimakon a yi ta faffaka da karafkiyar da ba za ta yi magani ba, kamar irin yadda ake kan yi a yanzu.
Lalachewar Tattalin Arziki
Tsare-tsaren tattalin arzikin da Shugaba Tinubu ya ƙaƙaba sun haifar da matsananciyar tsadar rayuwa a Najeriya, wadda ta haifar da ƙuncin rayuwa ga dukkan 'yan ƙasar nan. Albashin ma'aikata ko kuɗin haya ba ya iya biya, ballantana a kai ga sayen ruwa, wutar lantarki, abinci, sutura, kuɗin makarantar yara, da sauran ababen buƙatun yau da kullum na dole.
Tsadar abinci ta haddasa yunwa a cikin ƙasa. Masu jan akalar tattalin arziki a gwamnatin shugaba Tinubu sun yi makuwa, kuma sun rasa hanyar bi su koma bisa turba madaidaiciya. Ƙoƙarin su na lallai sai sun ramto kuɗaɗe da ƙara kuɗin ruwa da nufin ƙara wa Naira daraja, bai taɓa yin tasiri ba, kuma ba zai taɓa yin wani tasiri ba.
'Yan jagaliya ne kaɗai za su yi tunanin ƙara lafta wa 'yan Najeriya haraji fiye da ƙarfin aljifan su ne zai farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya, wanda tuni ya durƙushe.
Dawo da Tallafin Man Fetur
Gwamnatin Shugaba Tinubu ta dawo da biyan tallafin fetur a ɓoye, cikin sirri, wanda ta cire a ranar 29 ga Mayu, 2023. Tambaya ukku masu sauƙi a nan, shin me ya sa ba za a maida farashin litar fetur yadda take a baya ba, kafin a cire tallafin?
Shin an saka wannan kuɗaɗen tallafin mai da ake biya a kasafin kudin 2024? Kuma su wane ne 'yan-lelen gwamnati da ke amfana da kuɗaɗen tallafin?
Harajin Tsaron Intanet
Ƙoƙarin da Gwamnatin Shugaba Tinubu ke yi da nufin ƙaƙaba wa ‘yan Najeriya harajin tsaron intanet, ba wani abu ba ne sai kawai don ta ƙarfafa Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa na Musamman kan Harkokin Tsaro (ONSA), a kai shi wani matsayin da waɗanda suka tsara kundin tsarin mulkin Najeriya ba su yi tunanin kai ofishin ba.
Ai Majalisar Ƙasa ta lura da haka, a lokacin da ta yi fatali da ƙudirin neman ƙara wa Ofishin NSA ikon ƙirƙiro da wasu hukumomin tsaro.
Ƙoƙarin ƙirƙiro Harajin Tsaron Intanet na daga cikin wannan shiri da aka nemi yi, domin samun damar damfara maƙudan kuɗaɗe a Ofishin NSA, ta yadda zai zarce Ma'aikatar Harkokin Tsaro, Hukumomin Tsaro, Rundunar 'Yan Sandan Najeriya da Hukumomin kula da asirin chikin gida wato DSS da asirin waje wato NIA. Wannan kuwa zai kasance wani yunƙuri mai hatsarin gaske, wanda zai iya durƙusar da dimokraɗiyyar mu.
Ba zai yiwu mu ɗora iko ga wanda naɗin siyasa na Shugaban Ƙasa ne kan wanda al'umma suka zaɓa ba. A ƙirƙiri wasu kuɗaɗe da wani sunan tsaro to kamar ƙara masa ƙarfin ikon da bai cancanta ba ne.
Ya kamata mu koyi darasi daga tarihin abin da ya faru kan yadda J. Edgar Hoover ya zama Shugaban FBI mafi ƙarfin iko a Amurka, tsawon shekaru 48 da aka yi shugabanni 8 a Amurka.
Kwangila ta ɓarauniyar hanya
Tun da aka dawo mulkin dimokraɗiyya yau shekaru 25, ba mu taɓa ganin irin yadda aka yi ƙarfa-ƙarfar bayar da kwangila ta ɓarauniyar hanya, har ta Naira tiriliyan 15.6, sai a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu. An bayar da kwangilar ta gina titin Legas zuwa Kalaba ga babban abokin Tinubu, kuma abokin hada-hadar kasuwancin sa, ba bisa ƙa'idar da dokokin bayar da kwangila suka shimfiɗa ba. Wannan maƙudan kuɗaɗe za su iya gina dukkan titinan cikin Najeriya, har ma a rage canji mai yawa.
Tinubu ya fara shirin Takarar 2027
Tuni dai Shugaba Tinubu ya fara hawa bisa turbar sake tsayawa takara a 2027. Dalili kenan ya ke ta ƙara damfare manyan kayan yaƙin neman zaɓe, ta hanyar ci gaba da tatsar haraji daban-daban daga aljifan 'yan Najeriya.
Hakan ya nuna cewa ya na kakkafa wasu mazaɓu ne guda 5, waɗanda suka ƙunshi: 'Yan Majalisar Ƙasa wanda basu taka mashi birki, Gwamnoni, waɗanda ke jefa wa jama'ar su ɗan abincin tallafi domin su rufe bakin su, malaman addini, waɗanda suka goyi bayan tikitin 'Muslim-Muslim', sai Jami’an tsaro, waɗanda yake tunanin za su kare shi daga fushin hasalallun 'yan ƙasa.
Na ƙarshen su ne mawaƙan Hausa, waɗanda aka ɗauka domin suyi masa waƙoƙin kambamawa, da waƙoƙi waɗanda za su kawar kuma su shashantar, tare da ɗauke hankulan matasan Arewa daga raɗaɗin ciwon rayuwar ƙuncin da suke ciki a kullum.
Shugaba Tinubu bai damu da wahalar da ya jefa Jama’a ba
Abin takaici ne matuƙa idan aka yi la'akari da cewa halayyar da Shugaban Ƙasa ke nunawa, ta na ƙara bayyana irin rashin damuwar sa kan mawuyacin halin da ya jefa rayukan da dukiyoyin 'yan Najeriya. Kwata-kwata shi bai ma damu da halin da ake ciki ba.
Juyin Mulki a Jamhuriyar Nijar
Irin yadda Shugaba Tinubu ya nuna rashin a rikicin bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar cikin watan Yuli na 2023, shi ne ya janyo ficewar Ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso daga ECOWAS, lamarin da ya janyo barazana ga ɗorewar ƙungiyar, shekaru 49 bayan kafuwar ta. Ficewar waɗannan ƙasashe uku daga ECOWAS da kuma rungumar Rasha da suka yi, har ta girke sojoji a ƙasashen, da gaggawar son kafa sojoji da Amirka da Faransa ke yi a Najeriya, duk alamomi ne masu nuna kusantowar wata gagarimar matsala nan gaba.
Abin damuwa ne matuƙa, ganin cewa yayin da ƙasashen da Faransa ta rena suke ɓalle sarƙoƙin ƙangin bauta, shi kuma Shugaba Tinubu na Najeriya, a lokacin ya ke ƙara rufe idanu ya na tattago mana Faransa cikin ƙasar mu.
‘Yan Najeriya Sun Karaya da Gwamnatin Tinubu
'Yan Najeriya sun dawo daga rakiya da kuma sun daina yin amanna da gwamnatin Shugaba Tinubu, saboda ci gaba da azabtarwar da suke sha sakamakon tsadar rayuwa, rashin tsaro, cin hanci da rashawa, rashin aikin yi da jefa su cikin tarangahuma.
Su kuwa shugabanni, ko su kula, suna ci gaba da rayuwa a cikin bushasha, rashawa da almubazzaranci a kan idanun talakawa masu rayuwar ƙaƙa-ni-ka-yi.
Kammalawa
Mulkin Shugaba Buhari bala'i ne. Tsare-tsaren da ya bijiro da su sun jefa 'yan ƙasa cikin fatara da talauci, ya lalata tsarin tsaron ƙasa. Tinubuncin da ya ƙaƙaba da sunan gyara tattalin arziki, ya ƙara jefa 'yan ƙasa cikin jangwangwama. Ba tsari ba ne da ya yi daidai da dimokraɗiyya. Saboda haka ba za mu taɓa yin shiru ba. Ba kuma za mu yi shiru ba.
Usman Yusuf Farfesa ne, a Fannin Ilimin Cututtukan Kansa da na Jini da kuma Chanjin Ɓargo.