"Mun shiga Zaben Kananan Hukumomi kuma Muna fatan Nasara" - Ibrahim Galadima
- Katsina City News
- 20 May, 2024
- 476
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Alhaji Ibrahim Galadima shugaban riko na jam'iyyar PDP a karamar hukumar Katsina ya bayyana cewa; sun shiga zaben da za a gudanar na kananan hukumomin jahar Katsina a shekara mai kamawa kuma suna fatan samun nasara.
Galadima ya bayyana haka a lokacin zantawar sa da Manema labarai ranar Lahadi a gidansa da ke Goruba Road cikin garin Katsina. Shugaban rikon jam'iyyar ta PDP ya ce, "Mu ne jam'iyyar PDP tun a lokacin babu ta, yace K34 da KDF ne suka hadu sukai PDP a Katsina.
Galadima ya bayyana rikicin na cikin gida a jam'iyyar a matsayin wani abu da ake fatan ganin karshensa yace a dalilin haka ma uwar jam'iyya ta kasa ta kafa kwamiti akan duk inda ke da wata baraka a zauna don dun ke ta, yace kuma wanda aka shugabantar a kwamitin gogagge ne kowa yasan sanata Bukola Saraki.
Da yake taba batun zabe da za a gudanar na kananan hukumomi, Galadima yace suna da kyakkyawar fata akan zaben cewa PDP ce zata lashe shi, amma idan anbi gaskiya, yace idan kuma sunyi abinda suka saba kamar zaben da ya gabata wannan kuma dama sun saba.
A karshe Ibrahim Galadima ya yi kira ga 'ya'yan Jam'iyyar ta PDP a fadin jihar Katsina da cewa su kai zuciya nesa su hada kai don dunke duk wata baraka hakan zai kai ga jam'iyyar ga nasara a matakin karamar hukuma, jiha da ma kasa baki daya a lokacin zabuka masu zuwa.