An sanar da Mohammad Mokhbar a matsayin shugaban riƙon ƙwarya a Iran
- Katsina City News
- 20 May, 2024
- 576
Jagoran addinin ƙasar Iran, Ayatollah Khamenei ya sanar da Mohammad Mokhber a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na gwamnatin Iran.
Ya ce Mokhber zai hada kai da sauran bangarorin gwamnati - 'yan majalisa da kuma masu shari'a domin tabbatar da an gudanar da zaben sabon shugaban ƙasa.
Mokhbar zai riƙe muƙamin ne na watanni biyu kamar yadda tsarin mulkin ƙasar ta Iran ya zayyana, kafin sake gudanar da zaɓen shugaban ƙasar a cikin kwanaki 50.
Bisa sashe na 131 na kundin tsarin mulkin jamhuriyar ta Musulunci ta Iran, a yanayin mutuwa, mataimakin shugaba na ɗaya "tare da sahalewar jagorancin ƙasar, shi ne zai gaje shi, sannan daga bisani majalisar da ke kunshe da kakakin majalisar da shugaban sashen Shari'a da kuma mataimakin shugaban na farko za su shirya zaɓen sabon shugaban ƙasa, cikin kwanakin da ba su wuce 50 ba."
Kafin zamowa mataimakin shugaban ƙasa na ɗaya, Mohammad Mokhbar Dezfuli shi ne shugaban ma'aikatan Farman Imam, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin masu ƙarfin tattalin arziki a jamhuriyar Musulunci ta Iran, na kusan shekaru 15. Ita wannan cibiya tana aiki ne ƙarƙashin jagoran addini na jamhuriyar sannan kuma ba ta ƙarƙashin kowacce irin hukuma ko kuma ma'aikata.
Ya zamo mataimakin shugaban ƙasa ne bayan fafatawa da mutanen da suka yi suna a tsaurin aƙida sannan ya jagoranci cibiyar tattalin arzikin ƙasar domin samawa tattalin arzikin ƙasar makoma, duk da dai shaidu sun nuna bai samu cikakkiyar nasara ba.
Abin da muka sani game da shi
Shi ne mataimakin shugaban ƙasa na farko na jamhuriyar kuma na kusa da jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Ali Khamenei, kuma fitaccen mamba ne a majalisar gudanarwa ta Iran da jagoran juyin juya halin Musulunci ya naɗa, amma ba ya cikin wata jam'iyya.
An haife shi a shekara ta 1955 a birnin Dezful da ke lardin Khuzestan a kudu maso yammacin ƙasar. Yana da aure kuma yana da ’ya’ya biyu.
Mokhbar ya yi digirin farko a fannin injiniyan latroni, da digiri na biyu a fannin gudanarwa da tsare-tsare, sannan kuma ya yi digirinsa na uku a fannin shari’ar duniya.
Ya kasance fitaccen jami'in kare juyin juya halin Musulunci a lokacin yaƙin Iran da Iraki a shekarun 1980 zuwa 1988, kuma yana da "dogon tarihi na ayyukan juyin juya hali kafin nasarar juyin juya halin Musulunci a 1979, da tarihin gudanarwa bayan nasararsa," a cewarsa ga kamfanin dillancin labarai na Iran Tasnim.
A baya ya rike muƙamai da dama da suka hada da kula da sashen kiwon lafiya a garinsu,ya kuma yi mataimakin gwamnan Khuzestan, da shugaban wani banki mai zaman kansa.
Sannan ya koma gudanar da cibiyoyin kasuwanci da ke kusa da ofishin jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Ali Khamenei.
Tauraruwarsa ta fito ne bayan da ya zama shugaban kwamitin zartarwa a shekarar 2007, wanda ya shafi sarrafa kuɗaɗe da kadarorin da aka ƙwace daga gwamnatin Shah Mohammad Reza Pahlavi, kuma ya ci gaba da kasancewa a wannan matsayi har zuwa 2021.
Mohammad Mokhber ya kasance mataimakin shugaban ƙasar Iran na farko tun bayan naɗa shi a ranar 8 ga watan Agusta, 2021, bayan ya maye gurbin Eshaq Jahangiri, wanda shi ne tsohon mataimakin shugaban ƙasar Hassan Rouhani na farko.
A cikin watan Yulin 2010, Tarayyar Turai ta saka Mohamed Mokhber a cikin jerin sunayen jami'an gwamnati da ta kakaba wa takunkumi tare da zarginsa da hannu a "ayyukan makami mai linzami na nukiliya", kuma bayan shekaru biyu ya cire sunansa daga jerin.
An kuma sanya shi a cikin jerin takunkumin da ma'aikatar baitulmali ta Amurka ta a watan Janairun 2021. Washington ta fada a cikin jerin sunayen cewa kwamitin "yana da ruwa da tsaki a kusan kowane bangare na tattalin arzikin Iran, ciki har da makamashi da sadarwa da kuma sabis na kudi."
Ya kasance na kusa da shugaban Iran Ebrahim Raisi, kuma ya kasance mai bin diddigin batutuwan cikin gida da dama. Ya ziyarci ƙasashe da dama tare da sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa a fannoni daban-daban cikin shekaru biyu da suka gabata.
Mokhbar ya kuma kasance babban jami'i a cikin kungiyoyin kasuwanci
Daga shafin BBC Hausa