ANA ZARGIN WANI JAMI'IN TSARON AL'UMMA ( CWG) DA LAIFIN HARBIN UWA DA DANTA A BATSARI
- Katsina City News
- 18 May, 2024
- 471
Misbahu Ahmad
@ Katsina Times
Ana zargin wani jam'in tsaron al'umma (Katsina community watch corp) mai suna Basiru Kaura da laifin harbin wata mata mai suna Huzaifa Saminu da danta mai suna Ibrahim Saminu, a kauyen Yandaka dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jahar Katsina.
Lamarin ya faru ranar talata 13-05-2023 a cikin kauyen na Yandaka, inda shi jami'in community watch corp, Basiru Kaura yaje wajen Huzaifa Ibrahim ya nemi ta bashi rance ko bashi na kayan masaruhi da take sayarwa, sai tace ba zata ba shi ba saboda tana binshi bashi a baya. Kuma ta nemi ya biya ta amma ya ki ya biya ta, saboda haka tace ba zata kara masa ba sai ya biya ta.
Wani ganau, wanda ya nemi a sakaya sunanshi ya bayyana mana cewa, da matar ta hana shi bashin sai yace da ita idan bata bashi ba zai harbe ta.. Bayan yar gajeruwar gardama da ta barke tsakaninsu, sai Kaura ya ja da baya ya dirka masu bindiga ita da danta, Wanda nan take aka garzaya da su babbar asibitin Batsari domin ceto ranta.
Majiyarmu tace jami an CWG sun kama shi kuma yan sanda suna binciken lamarin, wadannan jami ai masu taimaka ma tsaro a yankuna ana samun bara gurbin cikin su na aikin da ba dai dai ba.
KATSINA TIMES
@ WWW.KATSINATIMES.COM
JARIDAR TASKAR LABARAI
WWW.JARIDARTASKARLABARAI.COM