AN KASHE KASURGUMIN "DAN TA ADDA USMAN MODI MODI DA MANYAN KWAMANDOJIN SHI
- Katsina City News
- 14 May, 2024
- 714
Muazu Hassan @Katsina Times
Wani fadan barayin daji a tsakaninsu ya kashe Babban dan ta addar nan da ya addabi mutanen Safana, Dutsinma, Batsari da kuma Dan Musa mai suna Usman Modi Modi tare da manyan kwamandojinshi su biyar.
Kamar yadda jaridun Katsina Times suka samu labari, Modi Modi ya jagoranci ya ranshi suka shiga jahar zamfara dabar wani barawo mai suna Alhaji Jika.suka kwaso masa shanu.
Akan hanyarsu ta dawowa sansanin su dake safana jahar Katsina, yaran Alhaji jika suka kwanta ma yaran Usman Modi Modi, suka kashe shi, tare da wasu kwamandajojinshi mai suna Harisu da Dogo jari, da lalu mai Dan Hannu, da Jae baki.
Majiyarmu tace, yaran Alhaji jika sun biyo daya daga cikin yaran Modi Modi mai suna Jan kare Wanda shine yayi gaba da wasu shanun, amma basu cim masa ba.
Modi Modi shine barawon da ya kashe gwarzon Dan sandan nan area kwamandan ACP Aminu Umar( Allah ya jikan shi) Wanda yayi ma mutanen yankin Dutsinma ta jahar Katsina aikin jarumta sosai.
Wani rahoton da mujallar Katsina city news ta buga ta watan febware 2024 inda ta kawo jadawalin duk yan ta addar da ke jahar Katsina.
Mujallar ta labarto Cewar an Haifi Usman Modi Modi a garin ummadau ta karamar hukumar safana.kuma yana da yara masu dauke da makai mutane dari biyu karkashin shi.
Labarin kashe Modi ya faranta mutanen yankin safana rai da murnar cewa in Allah ya yarda bana zasuyi noma.
Katsina Times @ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai @ www.taskarlabarai.com
All in All social media handles.
07043777779 0805777762