Kannywood Ta Naɗa Sanata Barau Shugaba Kuma Uba Ga Farfajiyar
- Katsina City News
- 12 May, 2024
- 483
Farfajiyar fina-finan Hausa Kannywood ta nada Sanata Jibrin Barau Shugaba kuma uba ga farfajiyar.
Farfajiyar ta karamma sanatan ranar Juma’a bayan ziyarar da suka kai wa dan majalisar a Abuja.
Bayan ya amince da naɗin da aka yi masa Barau ya tabbatar cewa zai ci gaba da mara wa farfajiyar da ‘yan fim baya domin ganin sun ci gaba.
Shugaban kungiyar Aktoci da na Kannywood Alhassan Kwalli ya kwatanta Sanatan a matsayin babban ginshiki da uba a gare su.
“Ka zama babban ginshiki a gare mu domin ka ci gaba da mara mana baya ba tun yanzu ba shekarun da dama da suka gabata a farfajiyar.
Bayan haka shugaban kwamitin amintattu na Kannywood Shehu Hassan-Kano, ya ce kungiyar a shirye ta ke ta hada kai da gwamnati domin bunkasa zaman lafiya da hadin kai a kasar nan.
Da yake mika godiyarsa ga aktocin Barau ya yi kira da su rika shirya fina-finan da za su taimaka wa gwamnati wajen samar da tsaro a kasan.
Ya ce Kannywood ta yi matukar bada gudunmawa, kuma ta na yi har yanzu, amma ya hore su da su cigaba da wayar wa mutane sanin mahimmancin zaman lafiya da kauce wa ayyukan ta’addanci a kasar nan.
” Gudunmawar da kuke badawa ba shi misaltuwa amma ina horonku ku ci gaba da kyawawan ayyukan da kuke yi domin mu samu ci daba mai dorewa a faɗin ƙasar nan.
Majiya: Premium Times Hausa