KASAR NIJAR :TSAKANIN HARIN ECOWAS DA MAKIRCIN TURAWAN YAMMA!!
- Katsina City News
- 17 Aug, 2023
- 952
KASAR NIJAR :TSAKANIN HARIN ECOWAS DA MAKIRCIN TURAWAN YAMMA!!
Gaba kura, baya siyaki
Daga Danjuma Katsina
Juyin mulkin kasar Nijar ya jefa ta cikin yanayi mafi sarkakiya a tarihin ta da kuma na yammacin Afrika.
Juyin mulki ne wanda soja marasa tsari da hangen nesa suka aiwatar da shi. Kuma ana ma iya kiran su dakikai. Kwarai kuwa! Dakikai mana, domin daga aiwatar da juyin mulkin suka danganta kansu da wata kasa, suka kuma nemi gudummuwar wata kungiyar sojan haya ta kasar Rasha.
Juyin mulki ne da aka yi shi ba domin dalilin ci gaban kasa ba, sai domin fushi na tsakanin dogari da wanda yake karewa, wanda akwai alamin kabilanci a cikin sa.
Ba na goyon bayan harin sojan ECOWAS a kasar Nijar, a maimakon haka ina goyon bayan a kara ma sojan kasarmu karfin gwiwa wajen fadan da suke yi da ’yan ta’addan cikin gida a bangarori daban-daban cikin Najeriya.
Amma ya kasar Nijar za ta kasance ko da babu harin ECOWAS? Shi kenan komai zai tafi daidai? Amsa ita ce, abin da kamar wuya, gurguwa da auren nesa, kuma a bene mai hawa goma.
Kidahuman sojan da suka kwace mulki da karfin bindiga a kasar, sun shelanta da aikata kusanta kansu da kasar Rasha, wadda yanzu haka take azabtar da kasashen yamma a yakin ta da kasar Ukraine.
Shin kasashen yamma za su kyale kasar Nijar ta tafi salun alun ga kasar rasha? A halin da ake ciki, wanda Amurka da sauran kasashen yamma da kawayen su suka yi ma Rasha taron dangi tana da karfin tattalin arziki da na soja da za ta iya bude wani fada da kalubale a kasar Nijar da Turawan yamma?
Sojan da suka amshi mulki a Nijar sun jefa kasar cikin gaba kura, baya siyaki. Ko dai, sojan ECOWAS su mayar da mulki ga gwamnatin da aka tube ta yakin da ba a san karshensa ba, in an fara shi, ko kuma matsin lamba da ’yan majalisun kasashen ECOWAS su hana a yi amfani da karfin soja, ECOWAS ta bar maganar.
Idan ECOWAS ta bar maganar, su kuma Turawan yamma su fito da nasu makircin ta nasu tsarin a kasar, wanda wannan ya fi muni, domin za su aiwatar da yakin basasa ne da sunkuru su hana kasar zaman lafiya. A lokacin kuma, kasar ta Nijar za ta ce za ta nemi ’yan’uwanta makwabta, musamman Najeriya domin a taimaka mata. Ko kuma a samu wasu soja masu kishi su sake canza gwamnatin domin daidaita al’amari, kada ya kara munana. Ko kuma su sojan da suka yi juyin mulkin su gane cewa, ramin da suke ciki na gafiya ne, ba ya fita; ba ramin kurege bane mai kofofi da yawa. Su hau teburin sulhuntawa na barin mulki, a ba su kariya.
Kasar Nijar ta dogara Kashi mafi yawa da kasashen waje,sai kawai suci gaba da bata abin da take so,duk da taki yin abin da suke so?
Ta kowace kafa, wasu soja sun jefa kasar Nijar a goran da babu fafi, kuma yana shafar yammacin Afrika da ma duniya baki daya.
Muhammad Danjuma
Shina mawallafin jaridun katsina Times da jaridar taskar labarai duk a bisa yanar gizo 07043777779 08057777862.