Tatsuniya: (11) Labarin Kurege Da Kura (Na Daya)

top-news

Tatsuniya: (11) Labarin Kurege Da Kura (Na Daya)

Ga ta nan, ga ta nanku.

Wata rana Kurege da Kura suna yawo, sai suka tsinci kyallen fatarí. Sai Kurege ya ce, bari ya je ya dinka musu riguna da shi.

Ya je ya dinko riguna biyu, amma girmansu daya. Ya bai wa Kura daya. Da Kura ta saka sai rigar ta matse ta, ta shake mata wuya saboda ta yi mata kadan.

Sai Kurege ya ce da Kura tun da rigar nan ta yi mata kadan, sai ta bar masa ita. Da Kura ta ji haka sai ta ce masa: "Da man ka cuce ni ne tun da ka dinka rigata daidai da taka, sai ka dauka."

Kurege ya hada duka biyun, suka shiga jeji don su farauto abin da za su ci. Da suka kamo namun daji da yawa sai suka dawo gindin wata bishiya, suna hutawa. Kurege yana so ya cinye naman shi kadai, amma ya rasa yadda zai yi. Can sai ya hango wasu 'yan mata a bakin rafi, 

sai ya dubi Kura ya ce:Ga yan mata can, mu je mu yi musu magana. Sai Kura ta yarda, suka je suka tarar da 'yan matan suna hira. Suka zauna suna sauraron hirar. Da Kurege ya ga hira ta fara yin dadi sai ya ce da Kura su je su dafa naman nasu. Sai Kura ta ce ita tana nan a wurin hira, ba za ta je ba.

Shi kuwa Kurege sai ya je domin ya dafa musu naman. Ashe ya sami abin da yake so, wato sai ya zabi nama mai kyau ya zuba a jakarsa, ya boye.

Sai ya samo naman mushe ya dafa, ya ajiye wa Kura. Bayan ta dawo sai ya mika mata nama. Kura ta hau ci ba ta san mushe ya dafa mata ba. Ta cinama, irin cin hadama, amma ta dan rage ta boye a jakarta. Kura ba ta da masaniyar cewa Kurege ya boye nama mai kyau, ya ba ta mushe. Saboda wayo irin na Kurege, sai ya dubi Kura ya ce: "Kura ki rage mini naman mana.

Saboda hadama irin ta Kura ita ma sai ta zan ba ka ba tun da kai ne ka dafa, na san sai da ka zabi inda ya fi ko'ina dadi ka ci ka koshi, ba zan kara maka ba.

Da rana bukka suka kwanta. Can cikin dare sai zawayi ya kama Kura. Ta nemi Kurege ya raka ta, sai ya ki, ya ce in zawayin yana damun ta, to ta fita waje. Ya kara da cewa:Idan ma abin ya dame ki ai sai ki yi shi a kwance ba sai kin tashi ba. Amma idan na ji ihu to babu lafiya, idan kuma abin ya yi tsanani, idan kuma kin ji shinu to lafiya ke nan." ta harari Kurege ta ce: "A'a ba Da rana ta fadi, kuma dare ya yi sai suka sami
Sai Kura ta fita waje ta yi kwanciyarta. Jim kadan sai kunama ta harbe ta, Kura da raki sai ta kwala kara, haka dai ta kwana tana zawo.

Wayewar gari ke da wuya, sai ta je ta fada wa Kurege cewa jiya da daddare kunama ta harbe ta. Sai Kurege ya ce: “Ai da ma mun yi da ke idan na ji shiru lafiya ta samu, idan kuma na ji ihu to ta yi tsanani sai in fita in taimaka miki." Bayan Kura ta ji bayanin Kurege, sai ta ce: To shi ke nan."

Da suka gama maganganunsu, sai Kurege ya rasa yadda zai yi ya dauki naman da ya boye ya kai gida, domin ya sani idan Kura ta gani za ta kwace. Sai ya yi dabara ya ba Kura shawara ta je ta sha ruwa, ta wanke jikinta kafin su tafi gida. Ba tare da zaton wani abu ba, sai ta kama hanya ta rafi.

Da Kurege ya ga ta tafi rafi, sai ya dauko namansa a inda ya boye, ya saka shi a jakar Kura, shi ma ya shiga cikin jakar. Da ta dawo daga wanka, sai ta dauki jakarta ta rataya. Ba ta san Kurege yana cikin jakar ba, sai ta kama hanya. Dadin waka ya sa ta kama hanyar gida ta fara tafiya, ta manta da Kurege. Tana cikin tafiya sai ta fara yi wa Jakarta waka tana cewa:

"Sai ni Kura durungu,
Na yi farauta,
Na cika jakata da nama,
Nama sai mun ture,
Ga shi a cikin jakata."

Haka ta rinka yi wa jakar waka. Sai da ta isa gida ta tuna ta bar Kurege a baya, sai ta ga ya kamata ta komna i nemansa. Sai ta ajiye jakarta ta juya ta kama hanyar komawa inda ta fito. Da Kurege ya ga ta tati, sai ya fita daga cikin jakar Kura, rike da namansa ya gudu zuwa gidansa.

Shi ya sa duk wanda ya je daji zai ga Kura tana ta yawon neman Kurege. Shi kuma da za ku je gidansa, za ku tarar da gidan cike yake da nama mai kyau, wanda yake ci ya more.

Kurungus.

Mun ciro wannan Labarin daga cikin littafi Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman