Tatsuniya (10): Labarin Wani Jarumin Sarki
- Katsina City News
- 18 Apr, 2024
- 634
Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wani jarumin sarki wanda a fagen yaki ba ya ja da baya. Duk inda ya sa gaba sai ya sami nasara. Yana da mata uku; amaryarsa kitse ne.
Sauran kuma mutane ne. To Sarkin nan ya fi son Takitsen. Duk lokacin da zai je yaki sai da ita yake tafiya.
Ana nan, sai wata rana wani yaki mai hadari da zafi ya taso. Sai ya yanke shawarar cewa wannan yakin ba irin wanda zai je da mata ba ne. Amma kuma yana tsoron barin amaryarsa a gida. Da sauran matansa biyu suka ji haka, sai suka ce ya bar ta a gida, babu komai za su kula da ita kamar yana nan. Sai ya amince da alkawarin da suka yi, ya hau shi da barade suka
dunguma zuwa filin daga, ya bar amaryarsa a gida.
Bayan tafiyar Sarki sai matan nan suka sa amarya girki. Tana nufar murhu sai ta narke saboda zafin wuta. Ganin haka fa sai suka fara kuka, suna cewa: "Takitse ta narke ta zama ruwa.
To da man akwai wani tsuntsu a gidan Sarki. Da ya ji abin da matan Sarki suke fada a cikin kuka. sai ya tashi ya nufi wajen yakin, yana cewa; Sarki, Sarki, Sarki ka mai da yaki baya, domin Takitse ta narke ta zama ruwa. haka ya yi ta yi, har Sarki ya kasa kunnesa, ya ji ana cewa ya bar yaki ya koma gida, domin matansa suna can a gida suna yin kuka.
Fadawa da baraden Sarki ma suka tsaya, suka ji abin da tsuntsu ke cewa. Sai ya tambaye Su abin da suka ji daga bakin tsuntsu, sai suka ce, ai Takitse amaryarsa ce ta narke. Nan da nan Sarki ya karya linzami, aka koma garinsa. Da ya isa fadar, sai ya shiga cikin turakarsa, ya sa Jakadiya ta kira matan, ya dube su ya ce Wace ce ta sa Takitse girki? Sai matar Sarki ta tsakiyar ta yi farat ta ce: "Uwar gida ce.
A fusace, Sarki ya umarci dogarawa su sare mata kai. Nan take suka flle mata kai.
Ba a wasa da umarnin Sarki.
Kurunkus.
Munciro wannan labarin daga Littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman.