YADDA DANKARAMI YA KASHE DANGOTE
- Katsina City News
- 08 Apr, 2024
- 778
Mu'azu Hassan
@ Katsina Times
Majiyoyi daban-daban sun tabbatar wa da jaridun Katsina Times cewa, lallai an kashe kasurgumin barawon nan mai dauke da muggan makamai da ke tsakanin dazuzzukan Batsari ta jihar Katsina da Dumburun ta jihar Zamfara.
Ganau a yankin dajin Dumburan sun fada wa jaridun Katsina Times cewa, a ranar Asabar 6 ga watan Afrilu 2024, wasu yaran Dankarami suka biyo kauyukan suna fada wa mutanen yankin cewa akwai fada da za a yi, amma su bar yankin, kuma ba ruwansu.
Yaran Dankarami sun je wani garken dabbobi na wan Dangote mai suna Sale suka kwashe masa dabbobi suka taho da su.
Da Sale ya ji labari, sai biyo dabbobinsa tare da wasu masu raka shi mutum 10. Suna tsakar tafiya sai yaran Dankarami suka kwanta masu suka tarwatsa su suka kashe wan Dangote mai suna Sale.
Yaran Sale da suka tsallake rijiya da baya daga kwantar baunar yaran Dankarami, sai suka koma suka fada wa Dangote abin da ya faru.
Dangote cikin fushi ya tattara yaransa wadanda ke kusa suka nufi inda aka kashe masa wa, tare da wani kanensa wanda suke kira da Abdo.
Kafin su Dangote su isa, Dankarami ya iso wani waje da manyan makamai da manyan yaransa sun yi wa wajen kwantar bauna a daidai wani daji da ke tsakanin Dumburun da iyakar karamar hukumar Batsari da Jibiya.
Dangote na tsakar tafiya cikin rukukin dajin, sai kawai yaran Dankarami suka auka masu da manyan bindigunsu masu yawa.
Majiyarmu ta ce ba tare da wani bata lokaci ba, yaran Dankarami suka yi nasara a kan na Dangote.
Dangote ya yi yunkurin gudu saboda duk musayar wutar da aka yi ba ta kama shi ba.
Majiyarmu ta ce, Dankarami da kansa ya je ya buge Dangote ya danne shi kasa ya fito da wata tsafaffiyar wuka ya yanke masa kai da ita.
Yaran Dangote suna ganin an kashe shugabansu, an kashe wani kanensa da suka taho tare, sai suka tarwatse suka dawo dabar Dangote suka ba da labari.
Wannan ya sa duk 'yan dabar Dangote kowa ya dau makamai aka nufi inda Dankarami yake. Nan aka yi ta bata-kashi.
Fadan ya kai kusan asubar farko. Daga baya sai ga jirgin saman yaki ya zo ya yi ta yi masu ruwan harsasai.
Wannan hari na sojan sama shi ne ya tsai da fadan kowa ya koma dabarsa.
Jirgin sama ya kashe mutanen kowane bangare masu yawan gaske.
Kisan Dangote yanzu ya sanya Dankarami shi ne barawo mafi karfi a wannan yankin.
Amma kisan sa yanzu zai bude wani sabon shafin fada tsakanin barayin Katsina da kuma na Zamfara.
J
Katsina Times @ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai @www.jaridartaskarlabarai.com
All in All social media handles.
07043777779