Ƴan bindiga sun sace mutum 26 a ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina
- Katsina City News
- 01 Apr, 2024
- 629
Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi awon gaba da mutum 26 a garin Ƙasai da ke ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne wajen ƙarfe 7:30 na safiyar Litinin ɗin nan, 1 ga watan Aprilun 2024 a lokacin da mutanen suka fita gonaki domin samo itace da karan dafa abinci.
Wani mazaunin yankin mai suna Suleiman Kasai wanda ya shaida ma Alfijir Radio cewa galibin mutanen da ƴan bindigar suka ɗauka ƙananan yara ne maza da mata.
Ya ce kaɗan ya rage adadin mutanen su fi haka, saboda wasu yaran sun shirya basu kai ga fita ba lamarin ya faru, wasu kuma suna hanyar tafiya suka ga ana gudu ƴan bindiga na bin mutane da gudu suka koma baya da gudu su ma.
Ya kuma ce akwai wani nasa cikin mutanen da ƴan bindigar suka sace. Inda ya ce Aƙwai ɗiyar yayarsa cikin mutanen da yan bindigar suka yi garkuwa da su.
Wannan ba shine karon farko da yan bindigar ke zuwa suna ɗaukar mana mutane ba. Watanni 2 da suka wuce ma sai da yan bindigar suka kashe mana mutum biyu, sannan suka tafi da wasu.
Yanzu mutum baya da ikon tafiya cikin gonaki wurin nemo makamashi face yan bindiga sun kai masa hari sun yi garkuwa da shi ," in ji Suleiman.
ƙaramar hukumar Batsari na cikin garuruwan da suke fama da matsalar tsaro a jihar Katsina inda ake sace mutane zuwa daji don neman kuɗin fansa.