Gwamnatin jihar Katsina ta biya diyya ga wadanda aikin Titin Kofar Soro zuwa Kofar Guga zai shafa
- Katsina City News
- 28 Mar, 2024
- 587
An biya diyya ga mutanen da aikin faɗaɗa titin Kofar Guga zuwa Kofar Soro zuwa tagwayen hanyoyi ya shafa a Katsina
Gwamnatin jihar Katsina ta ware sama da Naira miliyan 830 domin biyan diyya ga mutanen da za a taɓa gidaje da shagunsu wajen aikin faɗaɗa hanyar Ƙofar Guga zuwa Kofar Soro cikin garin Katsina.
Kwamishinan ƙasa da safiyo na jihar, Dr. Faisal Umar Kaita ne ya sanar da haka a lokacin da yake ƙaddamar da rabon chakin kuɗin diyyar ga mutanen da aikin faɗaɗa hanyar zai shafa yau Alhamis.
Kimanin mutane 331 ne gwamnatin za ta diyyar wajajensu domin faɗaɗa titin zuwa tagwayen hanyoyin saboda rage yawan cunkoso a birnin jihar
Dr Faisal Umar ya ce gwamnatin jihar Katsina ta biya mutane diyyar wajajensu ne domin ganin an fara aikin cikin lokaci kuma an gama da wuri.