Hukumar Tattara Kudaden Haraji ta Jihar Katsina ta Kaddamar da Shirin SIRTS don saukakawa masu Ababen hawa
- Katsina City News
- 25 Mar, 2024
- 512
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Hukumar Tattara Kudaden Haraji ta jihar Katsina bisa jagorancin Shugaban hukumar Alhaji Aminu Isiyaku ta Kaddamar da Shirin biyan haraji na hadin gwiwa ga Motocin 'yan Kasuwa Manya da Kanana a jihar Katsina mai suna, "Single Inter State Road Tax Sticker" (SIRTS), a takaice.
A ranar Alhamis 21 ga watan Maris ne Ofishin Tatattara Kudaden Haraji na jihar Katsina ya kaddamar da shirin Babban Ofishin jihar Katsina dake birnin Katsina, shirin wanda ya shafi Dukkanin Jihohin Nijeriya, katsina itace jiha ta Ashirin da uku da ta karbi shirin domin saukakawa masu ababen hawa yawan amsar Haraji a bisa hanya na babu gaira babu dalili tare da killacewa da kuma samar da hanyoyin kudin shiga na bai daya ga gwamnati.
Shirin zai takaita amsar kudin haraji na Kananan Hukumomi, Jihohi da duk wani haraji da ake dorawa masu Motocin haya wanda gwamnati bata san dashi ba.
A wajen kaddamar da shirin an bayyana cewa "Duk Direban da ya amshi Katin SIRTS na Shekara guda ba zai sake biya ba sai bayan wata shekarar, kuma an masa tsari mai sauki da kyau ta hanyar da hatta Talakawa zasu samu saukin kayan masarufi ga 'yan kasuwa duba da saukin Biyan Katin harajin na Shekara ga Direbobi, kuma Katin harajin zai cigaba da Amfani tun daga jihar Katsina zuwa ko wace jiha a Nijeriya duk daya ne, babu bambancin"
Katin yana dauke da dukkanin bayanai na Motar da Direbobin ke Tukawa, zuwa kuma sanya hannun hukumar Tattara kudin haraji ta jihar da aka yanki katin, kuma za'a iya tantance na Jabu, da na gaskiya ta hanyar haska shi da wayar salula ta hannun mutum, ko ta na'urar da hukumar ta tanada don binciken sahihancin sa.
A jihar Katsina an bayyana shiyoyi uku da za a cigaba da saida Katin wanda ya hada da shiyyar Katsin, Funtua da Daura. Kuma za a samar da shi, ga wakilai da hukumar ta amince da su, su zo su sayi Katin don isar da shi ga ko wane Diraban don takaita zirga-zirga.
Taron da aka gudanar na ranar Alhamis ta tattaro jami'an gwamnati, Jami'an tsaro da Hukumar kula da ababen hawa ta Road Safety, V.I.O, KASSAROTA, da sauran hukumomin da abin ya shafa.