Dangane da samun tsaiko akan aikin hanya da Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kaita da Jibia Hon. Sada Soli Jibia ya assasa ginawa.
- Katsina City News
- 02 Sep, 2023
- 713
Wadda zata taso daga kwanar yandaki, ta biyo cikin garin yandaki, tabi ta asibitin yandaki ta hade da sabuwar hanyar da ta taso daga Shinkafi zuwa Dankaba.
Da kuma wadda zata tashi daga hanyar Shinkafi zuwa Dankaba, tabi ta Kadafawa ta bule garin Kayauki ta hade da hanyar Katsina zuwa Daura.
Asalin aikin hanyar tun farko, Dan majalisar ya sanya shi a cikin kasafin kudin shekara ta 2022, amma kudin da aka saki na aikin a cikin kasafin kudin na 2022, ba zasu isa a kammala aikin ba.
Shiyasa Dan majalisar ya yi kokarin kara sanya aikin a cikin kasafin kudin shekarar da muke ciki ta 2023, wanda Dan majalisar ya yi bakin kokarin shi don ganin an sanya kudin an kuma sake su don ci gaba da aikin.
Hon. Sada Soli Jibia yanaso idan aka fara aikin ya tafi bai daya, ya kasance an kammala aikin kamar yadda aka tsara shi a cikin kasafin kudi, wannan shi ne dalilin samun tsaiko akan aikin.
Kawo yanzu an iya cewa haka ta cimma ruwa don bada jimawa ba, kafin shekarar nan da muke ciki ta kare yan kwangila da injiniyoyi tare da kayan aiki zasu dawo domin ci gaba da wannan aiki.
Hon. Sada Soli naba Al'ummar yankunan da aikin hanyar ya shafa hakuri, wannan tsaiko ba daga gareshi bane, sha'ani ne da ya shafi kasafin kudi da kuma tsare, tsaren Gwamnati duba da canjin Gwamnati da aka samu.
Amma yanzu komi ya tafi daidai, idan masu kwangilar aikin su ka dawo ba zasu tsaya ba, har sai sun kammala aikin baki daya, kamar yadda aka tsara shi a cikin kasafin kudi ma'ana ta taso daga kwanar yandaki har zuwa Kayauki.
01 September, 2023.