JAHAR ZAMFARA ZATA BIYA MA AIKATAN DA SUKAYI RITAYA
- Katsina City News
- 03 Mar, 2024
- 574
@ Katsina Times
Gwamnatin Jihar Zamfara ta tantance ma’aikata 3,079 da suka yi ritaya a ƙoƙarinta na biyan basukan da gwamnatocin baya suka bari.
Ma’aikatan jihar da na Ƙananan Hukumomi da suka yi ritaya a Zamfara ba su samu haƙƙoƙin su ba tun daga shekarar 2011, wanda kuɗaɗen suka taru tsawon shekaru.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa adadin ’yan fansho 1746 na ma'aikatan jiha da na Ƙananan Hukumomin jihar ne suka karɓi biya biyu na kaɗaɗen, wanda ya kai ma Naira Biliyan 2,312,841,065.08.
Sanarwar ta ƙara da cewa, kaso na biyu na kuɗaɗen garatuti na ’yan fansho ya fara ne a ranar Juma’ar da ta gabata, wanda ya kawo sauƙi da kwanciyar hankali ga rayuwar waɗanda suka yi ritayar, waɗanda suka shafe shekaru suna jiran haƙƙoƙinsu.
“An samu gagarumin ci gaba wajen tantance ’yan fansho na jiha da na Ƙananan Hukumomi. An fara biyan kaso na biyu na garatutin ’yan fansho da aka tantance a ranar Juma'a, 1 ga Maris, 2024.
“Jimillar 'yan fansho 413 da aka tantance daga jiha an biya su kuɗi kusan Naira 682,228,647.38 (miliyan ɗari shida da tamanin da biyu, dubu ɗari biyu da ashirin, da ɗari shida da arba’in da bakwai da naira talatin da takwas).
“Har ila yau, kaso na biyu na ’yan fansho da aka tantance daga Ƙananan Hukumomi, an biya mutum 403, wanda ya kai Naira 449,667,142.08 (miliyan ɗari huɗu da arba’in da tara, dubu ɗari shida da sittin da bakwai, naira ɗari da arba’in da biyu da kobo takwas).
“Daga cikin ’yan fansho 3079 da aka tantance, 1746 sun karɓi kuɗaɗen su a kashi biyu, waɗanda suka haɗa ga tsaffain ma'aikatan gwamnatin jiha da na Ƙananan Hukumomi. Adadin da aka biya ya zuwa yanzu dai ya kai Naira 2,312,841,065.08 (Biliyan biyu, miliyan ɗari uku da sha biyu, dubu ɗari takwas da arba'in da ɗaya da naira sittin da biyar da kwabo takwas).
“Har yanzu ana ci gaba da aiwatar da aikin tantance waɗanda suka yi ritayar, tare da biyan waɗanda aka riga aka tantance.”