Ziyarar Jam'iyyar APC: Tantance Ayyuka da Nazartar Zaben Kananan Hukumomi a jihar Katsina

top-news

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 

 KATSINA, 27 ga Fabrairu 2024 – A ranar Talata ne jam’iyyar APC reshen jihar Katsina karkashin jagorancin Alhaji Bala Abu Musawa ta cigaba da wani gagarumin rangadi a kananan hukumomin Katsina ta tsakiya da suka hada da Danmusa, Safana, Dutsinma, da Kurfi.  .

 Fitaccen jigo a jam’iyyar APC ta Jihar Katsina, Alhaji Bala Abu Musawa ya yi karin haske kan makasudin ziyarar, inda ya jaddada mayar da hankalinsu wajen tantance muhimman ayyukan da gwamnatin jihar Katsina, da kananan hukumomi, da shirin bunkasa ilimin 'Ya'ya mata na AGILE suka gudanar na hadin gwiwa.  A yayin rangadin, Alhaji Bala Abu Musawa ya bayyana muhimmancin duba ayyukan da ake gudanarwa, kamar gyaran makarantu, magudanar ruwa, gyaran hanyoyi, inganta Asibitoci, da dai sauransu.

 Bugu da kari, ya bayyana cewa kwamitin jam’iyyar APC na yin nazari sosai kan yadda za a gudanar da zaben kananan hukumomi da ke tafe.  Ziyarar na da nufin tantance alakar da ke tsakanin shugabannin kananan hukumomi da shugabannin jam’iyyar APC a matakin mazabu da kananan hukumomi.

 A ranar Alhamis, Alhaji Bala Abu Musawa ya mika sakon ban hakuri da jaje ga al’ummomin da hare-haren ta’addancin 'Yan bindiga ya shafa.  Ya kuma tabbatar wa da al’ummar jihar cewa gwamnatin jihar Katsina na aiki tukuru domin inganta tsaro a fadin jihar.  Da yake karkare jawabinsa, ya bukaci a ci gaba da baiwa Gwamna Malam Dikko Umaru Radda goyon baya, inda ya jaddada kudirin ciyar da jihar gaba zuwa ga nasarar da ba a taba samu ba.