ILMI NA CIKIN MURADAN GWAMNATIN LAWAL DARE
- Katsina City News
- 29 Feb, 2024
- 410
@ Katsina Times
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya ƙara jaddada cewa ilimi na ɗaya daga cikin ajandodi shida da ya sanya a gaba, ganin cewa ilimi ginshiƙin dukkan wayewa ne.
A lokacin gudanar da wani biki ranar Larabar nan a Gusau, Gwamna Lawal ya ƙaddamar da rabon kayan karatu da na koyarwa ga makarantun gwamnati, na Firamare da ƙaramar Sakandare guda 250 a duk faɗin jihar Zamfara.
Mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, a cikin wata sanarwa da ya fitar yau a Gusau, ya bayyana cewa an samo waɗannan kayan da aka raba ne daga Hukumar kula da ilimi bai-ɗaya ta 'Universal Basic Education Commission (UBEC)' da ke Abuja da kuma Hukumar kula da ƙananan yara ta duniya, UNICEF.
A cikin sanarwar, Kakakin Gwamnan ya yi ƙarin haske da cewa makarantu 250 ne za su amfana, wanda ya haɗa da littattafan karatu na matakai daban-daban guda 242,176, kayan wasa guda 200 don yara ƙanana masu matakin ECCDE, sai tebura da kujeru 25 na yaran ECCDE, sai kayan ɗakin karatu guda 8,210 da kuma na'urar UNICEF (NLP) guda 35 da waɗannan makarantu za su amfana da su.
Lokacin bikin wannan ƙaddamawar, Gwamnan ya nuna cewa a zamowar Zamfara mai fama da matsalar koma-baya a harkar ilimi, zai ci gaba da farauto agaji da masu neman haɗa hannu, don a samu haɓɓaka ilimi a jihar.
Gwamna Lawal ya ce, “Ina cike da farin cikin kasacewa ta cikin wannan taro na raba kayan karatu ga ɗaliban mu na ilimi. Wannan yana ɗaya daga cikin tagomashin da Zamfara ta amfana da su.
“Muna gudanar da cikakkunn gyare-gyare a makarantun Sakandare guda 60 a sassan jihar nan, a ƙarƙashin agajin Bankin Duniya na 'World Bank Assisted Community and Social Development Agency (CSDA).' Akwai makarantun Sakandare guda 6 a kowace Ƙaramar Hukuma da ake gudanar aikin gyaran, sai babban birnin jihar, Gusau da ke da makarantu 8.
“Dakar ta-ɓaci da aka ayyana a jihar nan, ba wai a Firamare ko Sakandare akwai abin ya tsaya ba, ya shafi hatta makarantun gaba da Sakandare. Yanzu haka ana ci gaba da gyaran kayan aiki, da samar da wasu sabbi a duk makarantun gaba da Sakandare da ke jihar nan.
“Wannan biki na yau, manuniya ce ta zo a lokacin da ya dace. Ta zo ta ƙara mana ƙarfi a ƙoƙarin mu na samar da ingantaccen ilimi a Zamfara, don tsamar da jama'ar mu daga cikin duhun jahilce da talauci."
Daga nan sai Gwamnan ya bayyana matakan da gwamnatin sa ta ɗauka don biyan bashin kuɗaɗen jabawar WAEC da NECO, waɗanda gwamnatocin jihar da suka shuɗe suka bari.
“Muna ƙoƙarin farfaɗo da ilimi a dukkan matakan karatu, don mu samar da turba mai kyau ga matasan mu. A yau, ɗaliban mu na rubuta jarabawar WAEC da NECO, kamar sauran 'yan uwan su da ke faɗin ƙasar nan, wanda kuma za a sakar masu sakamakon cikin lokaci.
"Mun sasanta da Hukumomin kula da gudanar da waɗannan jarabawoyi, har mun fara biyan bashin da muka gada, sakamakon gazawar gwamnatocin da suka gabata na kasa sauke wannan muhimmin nauyi.