Nijeriya ta yi tir da harin da ake kai wa 'yan jarida a Gaza, ta yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a rikicin Isra'ila da Falasɗinu .

top-news

Fim magazine

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi Allah-wadai da harin da sojojin Isra'ila ke kai wa 'yan jarida a rikicin da ke gudana a ƙasar Falasɗinu, yana mai jaddada cewa matakin na nuna take haƙƙin 'yan jarida da kuma haƙƙin ɗan'adam.

A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai ga Ministan, Rabi'u Ibrahim, ya ce Idris ya bayyana hakan ne a jawabin sa a Taro na Musamman na Ministocin Yaɗa Labarai na Ƙasashen Musulmi mai taken: “Bayar Da Labarin Ƙarya Da Kuma Kisan ‘Yan Jarida Da Gwamnatin Isra’ila ke yi a Lokacin Mamayar da Isra'ila ta yi wa Falasɗinu,” wanda aka gudanar a ranar Asabar, 24 ga Fabrairu, 2024 a birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya.

Ministan, wanda ya samu wakilcin Shugaban Ofishin Jakadancin Nijeriya a ƙasar Turkiyya, Ambasada Zayyad Abdul-Salam, ya bayyana cewa tun farkon rikicin, ‘yan jarida na ta fuskantar matsantawa, tsoratarwa da tashin hankali, har ma da kisa saboda kawai suna gudanar da aikin su na sanar da jama'a da kiyaye ƙa'idojin gaskiya da adalci.

Ya ce: “Daga ƙididdigar da Kwamitin Kare Haƙƙin ‘Yan Jarida na duniya (CPJ) ya bayar, an kashe ‘yan jarida da ma’aikatan kafafen watsa labarai kusan tamanin da takwas tun lokacin da aka fara yaƙin a ranar 7 ga Oktoba, 2023.

“A matsayin mu na Ministocin Yaɗa Labarai da ke wakiltar ƙasashe a Ƙungiyar Ƙasashen Musulunci, ya zama wajibi a gare mu da mu yi Allah-wadai da irin wannan ta’asa da tauye haƙƙin ‘yan jarida da ke gudanar da ayyukan su a Falasɗinu. 

"Dole ne mu tsaya tsayin daka don goyon bayan abokan aikin mu na kafafen yaɗa labarai waɗanda suke sadaukar da rayukan su a kullum don bayar da rahoton rikici a Falasɗinu wacce aka mamaye da kuma ba da murya ga marasa murya.”

Idris, wanda ya buƙaci takwarorin sa a ko da yaushe da su dage kan ganin an tabbatar da gaskiya a kowane lokaci ta hanyar neman yanayi mai kyau don bai wa 'yan jarida damar gudanar da ayyukan su, ya yi tir da duk wani yunƙuri na karkatar da gaskiya tare da rashin bayyana haƙiƙanin halin da mutane ke ciki a Falasɗinu.

Ya shawarci ministocin da ke halartar taron da su binciko dabarun sadarwa, goyon baya, da haɗin gwiwa don faɗaɗa muryar ‘yan jarida waɗanda ke da ƙarfin halin tattara bayanan take haƙƙin bil’adama da cin zarafi da ake yi wa al’ummar Falasɗinu.

Ya ce: “Babban martanin mu dole ne ya kasance sadaukarwa don kiyaye ƙa’idojin ‘yancin ‘yan jarida, ‘yancin faɗin albarkacin baki, da ‘yancin samun bayanai. Waɗannan muhimman haƙƙoƙin ɗan'adam waɗanda ke cikin dokokin ƙasa da ƙasa sun zama ginshiƙan dimokiraɗiyya da kyakkyawan shugabanci. 

"Ba za mu ƙyale waɗanda ke neman su murƙushe saɓanin ra'ayi su tattake su kuma su sarrafa labarin ba.” 

Ministan ya yi kira da a tsagaita buɗe wuta cikin gaggawa a Gaza kuma ya jaddada matsayin Nijeriya kan samar da ƙasashe biyu don magance rikicin Falasɗinu, da tabbatar da an mutunta haƙƙi da 'yancin al'ummar Falasɗinu da Isra'ila.