ƳAN BINDIGA SUN KAI MUMMUNAN HARI NAHUTA TA BATSARI
- Katsina City News
- 18 Feb, 2024
- 655
Misbahu Ahmad @Katsina Times
Ƴan bindiga ɗauke da miyagun makamai sun kai hari ƙauyen Nahuta dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Da misalin ƙarfe 07:30pm na daren ranar Asabar 17-02-2024 ƴan bindiga suka afka ma ƙauyen Nahuta, kamar yadda wani mazauni garin ya bayyana mana, ɓarayin sun kashe mutum biyu macce ɗaya namiji ɗaya: Badiya Bawa da Nura Isma Salihawa. Ya ƙara da cewa tuni anyi zana'izarsu kamar yadda addinin musulunci ya tanada. Sannan sun harbi mutune huɗu kuma tuni aka garzaya da su aaibitin Batsari domin yi masu magani.
Bayan wannan ta'addanci da suka aikata, ɓarayin na daji, sun yi garkuwa da mutane masu yawa amma wasu daga cikin su sun kuɓuta, saidai ya zuwa haɗa rahotonnan mutane biyar ke hannunsu. Kuma sun sace dabbobi masu yawa ma ƙauyen, sun ɓalle shaguna sun yi awon gaba da kayayyakin masaruhi da wayoyin hannu.
Harin ƴan bindiga a ƙauyen Nahuta ba baƙon al'amari ba ne, domin in baa manta ba, ɓarayin sun kai hari sansanin jami'an tsaro dake aikin bada tsaro a Nahuta ranar lahadi 14-01-2024 har suka ƙona motoci biyu na jami'an tsaron.