Da Ɗuminsa: Ku dauki mataki kan duk yan kasuwar dake ɓoye abinci - Tinubu ya umurci jami'an tsaron Nijeriya
- Katsina City News
- 15 Feb, 2024
- 399
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da a duba yiwuwa kafa rundunar ‘yansandan jihohi a kasar.
Wannan dai na daga cikin batutuwan da aka tattauna a wajen wani taron gaggawa da ya yi da gwamnonin jihohin kasar 36 ranar Alhamis a fadarsa.
Taron dai ya mayar da hankali ne kan nazarin muhimman matsalolin da ke addabar kasar yanzu da zimman nemo bakin zaren warware su.
Batutuwan dai sun hada da na tsaro, da tsadar rayuwan da karancin abinci da makamantansu kamar yadda ministan watsa labarai da wayar da kan jama’a Mohammed Idris ya sanar da manema labarai bayan tashi daga zaman.
Ya ce zaman ya kunshi shawarwari kan yadda za a hada kai tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya domin magance matsalolin da ke ci wa kasar tuwo a kwarya.
''Ba ma son rabe-rabe tsakanin jihohi da gwmnatin tarayya, ko da a wace jam'iyya kake, an yi shawawara kan yadda za a ciyar da kasar gaba'', in ji shi.
Dangane da 'yan sandan jihohi, ministan ya ce shugaba Tinubu ya amince cewa a duba maganar yiwuwar kafa 'yan a fadin jihohin kasar, maimakon dogara da 'yan sandan gwamnatin tarayya.
''To sai dai wani abu ne da yake bukatar nutsuwa a duba a kuma tantance, ba abu ba ne da kawai za a fada cikinsa kai tsaye, yana bukatar nazari sosai'', in ji ministan yada labaran.
Ministan ya kara da cewa taron ya amince da shugabannin hukumomin tsaron kasar su yi aiki tare da gwamnonin jihohi wajen sa kafar wando daya da wadanda suka boye kayan abinci da muhimman kayan masarufi domin su yi tsada sannan su sayar da su.
Hka kuma shugaban kasar da gwamnonin sun kuma amince cewa kasar ba ta bukatar shigo da kayan abinci daga waje, domin sauko da farashinsa, suna masu cewa kasar na iya dogara da abincin da al’ummarta ke nomawa.
Wannan taron dai na zuwa ne ‘yan kwanakki bayan da gwamnonin babbar jam’iyyar adawa ta PDP suka yi wani taron inda suka kwatanta halin da kasar ta shiga ta fuskar tabarbarewar tattalin arziki da tashin farashin kaya da rashin tsaro da irin wanda kasar Venezuela ta shiga a shekarun baya, BBC Hausa ce ta rawaito
Ko a jiya ma dai majalisar sarakunan gargajiya ta kasar ta yi wani taro Kaduna a inda ta nuna damuwa game da karuwar matsalolin tsaro da talauci da kuma rashin aikin yi tsakanin al’ummar kasar musamman a yankin na arewa.