ƁARAYIN DAJI SUN KAI HARI GARIN ƘASAI TA BATSARI
- Katsina City News
- 13 Feb, 2024
- 633
Misbahu Ahmad Batsari
@ Katsina Times
Ɓarayin daji masu satar dabbobi da garkuwa da mutane sun kai hari Ƙasai ta ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
A ranar litanin da misalin ƙarfe 07:30pm na dare wasu mahara suka kai harin, inda suka kutsa cikin garin suka kashe mutune biyu, sannan suka shiga wani shagon caji suka sace wayoyin hannu (cell phone), sannan suka gudu ba tare da samun wata tirjiya ba.
Lamarin tsaro na ƙara taɓarɓarewa a yankin Batsari domin ko a ranar lahadi sai da ɓarayin suka kai hari hanyar Batsari zuwa jibia inda suka kashe mutane takwas. Sannan a kwanakin baya ɓarayin sun kai hari garin na Ƙasai, inda suka sace mutane 7 waɗanda har yanzu basu sake su ba.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779 08057777762